\id SNG - Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ \ide UTF-8 \h Waƙar Waƙoƙi \toc1 Waƙar Waƙoƙi \toc2 Waƙar Waƙoƙi \toc3 WW \mt1 Waƙar Waƙoƙi \c 1 \p \v 1 Waƙar Waƙoƙin Solomon. \b \sp Ƙaunatacciya\f + \fr 1.2 \fr*\ft Da farko dai an nuna masu magana ko namiji ko ta mace bisa ga jinsi na wakilan sunayen da Ibraniyanci suka yi amfani da su, a gefen shafi ta wurin salon \ft*\fqa Ƙaunatacce \fqa*\ft da \ft*\fqa Ƙaunatacciya \fqa*\ft daki-daki. An nuna sauran kalmomin da \ft*\fqa Abokai. \fqa*\ft A waɗansu wurare akwai shakka game da ɓangarori da salo.\ft*\f* \q1 \v 2 Bari yă sumbace ni da sumbar bakinsa, \q2 gama ƙaunarka ta fi ruwan inabi zaƙi. \q1 \v 3 Ƙanshin turarenka mai daɗi ne; \q2 sunanka kuwa kamar turaren da aka tsiyaye ne. \q2 Shi ya sa mata suke ƙaunarka! \q1 \v 4 Ka ɗauke ni mu gudu, mu yi sauri! \q2 Bari sarki yă kai ni gidansa. \sp Ƙawaye \q1 Muna farin ciki muna kuma murna tare da kai, \q2 za mu yabi ƙaunarka fiye da ruwan inabi. \sp Ƙaunatacciya \q1 Daidai ne su girmama ka! \b \q1 \v 5 Ni baƙa ce, duk da haka kyakkyawa. \q2 Ya ku ’yan matan Urushalima, \q2 ni baƙa ce kamar tentunan Kedar, \q2 kamar labulen tentin Solomon.\f + \fr 1.5 \fr*\ft Ko kuwa \ft*\fqa Salma\fqa*\f* \q1 \v 6 Kada ku harare ni domin ni baƙa ce, \q2 gama rana ta dafa ni na yi baƙa. \q1 ’Ya’yan mahaifiyata maza sun yi fushi da ni \q2 suka sa ni aiki a gonakin inabi; \q2 na ƙyale gonar inabi na kaina. \q1 \v 7 Faɗa mini, kai da nake ƙauna, ina kake kiwon garkenka \q2 kuma ina kake kai tumakinka su huta da tsakar rana. \q1 Me ya sa zan kasance kamar macen da aka lulluɓe \q2 kusa da garkunan abokanka? \sp Ƙawaye \q1 \v 8 Ke mafiya kyau a cikin mata, in ba ki sani ba, \q2 to, ki dai bi labin da tumaki suke bi \q1 ki yi kiwon ’yan awakinki \q2 kusa da tentunan makiyaya. \sp Ƙaunatacce \q1 \v 9 Ina kwatanta ke ƙaunatacciyata, da goɗiya \q2 mai jan keken yaƙin kayan Fir’auna. \q1 \v 10 ’Yan kunne sun ƙara wa kumatunki kyau, \q2 wuyanki yana da jerin kayan wuya masu daraja. \q1 \v 11 Za mu yi ’yan kunnenki na zinariya, \q2 da adon azurfa. \sp Ƙaunatacciya \q1 \v 12 Yayinda sarki yake a teburinsa, \q2 turarena ya bazu da ƙanshi. \q1 \v 13 Ƙaunataccena yana kamar ƙanshin mur a gare ni, \q2 kwance a tsakanin ƙirjina. \q1 \v 14 Ƙaunataccena kamar tarin furanni jeji ne gare ni \q2 daga gonakin inabin En Gedi. \sp Ƙaunatacce \q1 \v 15 Ke kyakkyawa ce, ƙaunatacciyata! \q2 Kai, ke kyakkyawa ce! \q2 Idanunki kamar na kurciya ne. \sp Ƙaunatacciya \q1 \v 16 Kai kyakkyawa ne, ƙaunataccena! \q2 Kai, kana ɗaukan hankali! \q2 Gadonmu koriyar ciyawa ce. \sp Ƙaunatacce \q1 \v 17 Al’ul su ne ginshiƙan gidanmu; \q2 fir su ne katakan rufin gidanmu. \c 2 \sp Ƙaunatacciya\f + \fr 2.1 \fr*\ft Ko kuma \ft*\fqa Ƙaunatacce\fqa*\f* \q1 \v 1 Ni furen bi-rana ne na Sharon, \q2 furen bi-rana na kwari. \sp Ƙaunatacce \q1 \v 2 Kamar furen bi-rana a cikin ƙayayyuwa \q2 haka ƙaunatacciyata take a cikin ’yan mata. \sp Ƙaunatacciya \q1 \v 3 Kamar itacen gawasa a cikin itatuwan jeji \q2 haka ƙaunataccena yake a cikin samari. \q1 Ina farin ciki in zauna a inuwarsa, \q2 ’ya’yan itacensa suna da daɗin ɗanɗanon da nake so \q1 \v 4 Ya kai ni babban zauren da ake liyafa, \q2 ƙauna ita ce tutarsa a gare ni. \q1 \v 5 Ka ƙarfafa ni da zabibi \q2 ka wartsake ni da gawasa, \q2 gama ina suma don ƙauna. \q1 \v 6 Hannunsa na hagu yana a ƙarƙashin kaina, \q2 hannunsa na dama kuma ya rungume ni. \q1 \v 7 ’Yan matan Urushalima, ku yi mini alkawari \q2 da bareyi da ƙishimai na jeji. \q1 Ba za ku tā da ko ku farka ƙauna ba \q2 sai haka ya zama lalle. \b \q1 \v 8 Saurara! Ƙaunataccena! \q2 Duba! Ga shi ya iso, \q1 yana tsalle a duwatsu, \q2 yana rawa a bisa tuddai. \q1 \v 9 Ƙaunataccena yana kama da barewa ko sagarin ƙishimi \q2 Duba! Ga shi can tsaye a bayan katangarmu, \q1 yana leƙe ta tagogi, \q2 yana kallo ta cikin asabari. \q1 \v 10 Ƙaunataccena ya yi magana ya ce mini, \q2 “Tashi, ƙaunatacciyata, \q2 kyakkyawata, ki zo tare da ni. \q1 \v 11 Duba! Damina ta wuce; \q2 ruwan sama ya ɗauke ya kuma ƙare. \q1 \v 12 Furanni sun hudo a duniya; \q2 lokaci yin waƙa ya zo, \q1 ana jin kukan kurciyoyi \q2 ko’ina a ƙasarmu. \q1 \v 13 Itacen ɓaure ya fid da ’ya’yansa da sauri; \q2 tohon inabi suna ba da ƙanshinsu. \q1 Tashi, zo, ƙaunatacciyata; \q2 kyakkyawata, zo tare da ni.” \sp Ƙaunataccena \q1 \v 14 Kurciyata a kogon dutse, \q2 a wuraren ɓuya a gefen dutse, \q1 nuna mini fuskarki, \q2 bari in ji muryarki; \q1 gama muryarki da daɗi take, \q2 fuskarki kuma kyakkyawa ce. \q1 \v 15 Kama mana ɓeraye, \q2 ƙananan ɓerayen \q1 da suke lalatar da gonakin inabi, \q2 gonakin inabinmu da suke cikin yin fure. \sp Ƙaunatacciya \q1 \v 16 Ƙaunataccena nawa ne ni kuma tasa ce; \q2 yana kiwon garkensa a cikin furannin bi-rana. \q1 \v 17 Sai gari ya waye \q2 inuwa kuma ta watse, \q1 ka juye, ƙaunataccena, \q2 ka zama kamar barewa \q1 ko kamar sagarin ƙishimi \q2 a kan tuddai masu ciyawa. \b \c 3 \q1 \v 1 Dare farai a kan gadona \q2 na nemi wanda zuciyata take ƙauna; \q2 na neme shi amma ban same shi ba. \q1 \v 2 Zan tashi yanzu in zagaya gari, \q2 in ratsa titunansa da dandalinsa; \q1 zan nemi wanda zuciyata take ƙauna. \q2 Saboda haka na neme shi, amma ban same shi ba. \q1 \v 3 Masu tsaro suka gamu da ni \q2 yayinda suke kai kawo a cikin birni, sai na ce, \q2 “Kun ga mini wanda zuciyata take ƙauna?” \q1 \v 4 Rabuwata da su ke nan \q2 sai na sami wanda zuciyata take ƙauna. \q1 Na riƙe shi, ban yarda yă tafi ba \q2 sai da na kawo shi gidan mahaifiyata, \q2 zuwa ɗakin wadda ta yi cikina. \q1 \v 5 ’Yan matan Urushalima, ku yi mini alkawari \q2 da bareyi da ƙishimai na jeji. \q1 Ba za ku tā da ko ku farka ƙauna ba \q2 sai haka ya zama lalle. \b \q1 \v 6 Wane ne wannan mai zuwa daga hamada \q2 kamar tunnuƙewar hayaƙi, \q1 cike da ƙanshin turaren mur da lubban \q2 da aka yi da kayan yajin ’yan kasuwa? \q1 \v 7 Duba! Abin ɗaukar Solomon ne, \q2 jarumawa sittin suke rakiya, \q2 zaɓaɓɓun sojojin Isra’ila, \q1 \v 8 dukansu suna saye da takobi \q2 dukansu ƙwararru ne a yaƙi, \q1 kowanne da takobinsa a rataye a gefensa, \q2 a shirye don abubuwan bantsoro na dare. \q1 \v 9 Sarki Solomon ya yi wa kansa abin ɗauka; \q2 ya yi shi da katako daga Lebanon. \q1 \v 10 An yi sandunansa da azurfa, \q2 aka yi ƙasarsa da zinariya. \q1 An lulluɓe wurin zaman da zanen shunayya, \q2 ’yan matan Urushalima sun yi mata irin yayen da ake yi na ƙauna. \q1 \v 11 Fito, ku ’yan matan Sihiyona, \q2 ku ga Sarki Solomon yana saye da rawani, \q2 rawanin da mahaifiyarsa ta naɗa masa, \q1 a ranar aurensa, \q2 a ranar da zuciyarsa ta yi farin ciki. \c 4 \sp Ƙaunatacce \q1 \v 1 Ke kyakkyawa ce, ƙaunatacciyata! \q2 Kai, ke kyakkyawa ce! \q2 Idanunki sun yi kamar na kurciya a cikin lulluɓinki. \q1 Gashinki ya yi kamar garken awaki \q2 da suke gangarawa daga Dutsen Gileyad. \q1 \v 2 Haƙoranki sun yi kamar garken tumakin da ba a daɗe da yin musu sausaya ba, \q2 da suke haurawa daga inda aka yi musu wanka. \q1 Kowanne yana tare da ɗan’uwansa; \q2 babu waninsu da yake shi kaɗai. \q1 \v 3 Leɓunanki kamar zaren jan garura \q2 bakinki yana da kyau. \q1 Kumatunki sun yi kamar rumman \q2 da aka tsaga biyu a cikin lulluɓinki. \q1 \v 4 Wuyanki ya yi kamar hasumiyar Dawuda, \q2 da aka gina da daraja; \q1 a kansa an rataye garkuwoyi dubu, \q2 dukansu garkuwoyin jarumawa ne. \q1 \v 5 Nonanki biyu sun yi kamar bareyi biyu, \q2 kamar tagwayen barewa \q2 da suke kiwo a cikin furen bi-rana. \q1 \v 6 Sai gari ya waye \q2 inuwa kuma ta watse, \q1 zan je dutsen mur \q2 da kuma tudun turare. \q1 \v 7 Duk, ke kyakkyawa ce, ƙaunatacciyata; \q2 babu wani lahani a cikinki. \b \q1 \v 8 Ki tare da ni daga Lebanon, amaryata, \q2 zo tare da ni daga Lebanon. \q1 Ki gangara daga ƙwanƙolin Amana, \q2 daga ƙwanƙolin Senir, ƙwanƙolin Hermon, \q1 daga ramin zaki \q2 da kuma dutsen da damisoshi suke zama. \q1 \v 9 Kin saci zuciyata, ’yar’uwata, amaryata; \q2 kin saci zuciyata \q1 da hararar idanunki, \q2 da dutse mai daraja guda na abin wuyanki. \q1 \v 10 Ƙaunarki abar farin ciki ne, ’yar’uwata, amaryata! \q2 Ƙaunarki ta fi ruwan inabi gamsuwa, \q2 ƙanshin turarenki kuma ya fi duk wani kayan yaji! \q1 \v 11 Leɓunanki suna zub da zaƙi kamar kakin zuma, amaryata; \q2 madara da zuma suna a ƙarƙashin harshenki. \q2 Ƙanshin rigunanki ya yi kamar na Lebanon. \q1 \v 12 Ke lambu ne da aka kulle, ’yar’uwata, amaryata; \q2 ke maɓulɓula ce da aka kewaye, maɓulɓular da aka rufe. \q1 \v 13 Shuke-shukenki gonar rumman ne \q2 da ’ya’yan itace masu kyau \q2 na lalle da nardi, \q2 \v 14 nardi, da asfaran, \q2 kalamus, da kirfa, \q2 da kowane irin itacen turare, \q2 da mur da aloyes \q2 da kuma dukan kayan yaji masu kyau. \q1 \v 15 Ke lambun maɓulɓula ne, \q2 rijiya mai ruwan da yake gudu \q2 yana gangarawa daga Lebanon. \sp Ƙaunatacciya \q1 \v 16 Farka, iskar arewa, \q2 ki kuma zo, iskar kudu! \q1 Hura a kan lambuna, \q2 don ƙanshinsa yă bazu har waje. \q1 Bari ƙaunataccena yă zo cikin lambunsa \q2 yă ɗanɗana ’ya’yan itacensa mafi kyau. \c 5 \sp Ƙaunatacce \q1 \v 1 Na zo lambuna, ’yar’uwata, amaryata; \q2 na tattara mur nawa da kayan yajina. \q1 Na sha zumana da kuma kakinsa \q2 na sha ruwan inabina da kuma madarana. \sp Ƙawaye \q1 Ku ci, ku kuma sha, ya ku ƙawaye; \q2 ku sha ku ƙoshi, ya ƙaunatattu. \sp Ƙaunatacciya \q1 \v 2 Na yi barci amma zuciyata tana a farke. \q2 Ku saurara! Ƙaunataccena yana ƙwanƙwasa ƙofa. \q1 “Buɗe mini, ’yar’uwata, ƙaunatacciyata, \q2 kurciyata, marar laifina. \q1 Kaina ya jiƙe da raɓa, \q2 gashina ya yi danshin ɗiɗɗigar dare.” \q1 \v 3 Na tuɓe rigata, \q2 sai in sāke sa ta kuma? \q1 Na wanke ƙafafuna, \q2 sai in sāke ɓata su? \q1 \v 4 Ƙaunataccena ya turo hannunsa ta cikin ramin ƙofar; \q2 zuciyata ta fara juyayi a kansa. \q1 \v 5 Na tashi don in buɗe wa ƙaunataccena, \q2 sai hannuna ya jiƙe sharkaf da mur, \q1 yatsotsina suna ɗiga da mur, \q2 a hannuwan ƙofar. \q1 \v 6 Na buɗe wa ƙaunataccena ƙofa, \q2 amma ƙaunataccena ba ya nan, ya riga ya tafi. \q1 Zuciyata ta damu da tafiyarsa. \q1 Na neme shi amma ban same shi ba. \q2 Na yi ta kiransa amma bai amsa ba. \q1 \v 7 Masu gadi suka gamu da ni \q2 yayinda suke kai kawo a cikin birni. \q1 Suka yi mini dūka, suka yi mini rauni; \q2 suka ƙwace gyalena \q2 waɗannan masu gadin katanga! \q1 \v 8 ’Yan matan Urushalima, ina roƙonku, \q2 in kun sami ƙaunataccena \q1 me za ku ce masa? \q2 Ku ce masa na suma saboda ƙauna. \sp Ƙawaye \q1 \v 9 Mafiya kyau a cikin mata \q2 me ya sa ƙaunataccenki ya fi sauran? \q1 Don me kike roƙonmu mu faɗa masa yadda kike ji? \sp Ƙaunatacciya \q1 \v 10 Ƙaunataccena kyakkyawa ne ƙaƙƙarfa kuma, \q2 da ƙyar a sami irinsa ɗaya a cikin dubu goma. \q1 \v 11 Kansa zinariya ce zalla; \q2 gashinsa dogaye ne \q2 baƙi wuluk kamar hankaka. \q1 \v 12 Idanunsa sun yi kamar na kurciyoyin \q2 da suke kusa da ruwan rafi, \q1 da aka wanke da madara \q2 aka kuma kafa kamar kayan ado masu daraja. \q1 \v 13 Kumatunsa kamar lambun kayan yaji \q2 suna ba da turare. \q1 Leɓunansa sun yi kamar furen bi-rana \q2 suna ɗiga da mur. \q1 \v 14 Hannuwansa kamar sandunan zinariyar \q2 da aka sa musu duwatsu masu daraja. \q1 Jikinsa ya yi kamar gogaggen hauren giwan \q2 da aka yi masa ado da duwatsun saffaya. \q1 \v 15 Ƙafafunsa sun yi kamar ginshiƙan dutsen alabastar \q2 da aka kafa su a cikin rammukar zinariya. \q1 Kamanninsa ya yi kamar Lebanon, \q2 mafi kyau kamar itacen al’ul nasa. \q1 \v 16 Bakinsa zaƙi ne kansa; \q2 komensa yana da kyau. \q1 Haka ƙaunataccena, abokina, yake \q2 ’yan matan Urushalima. \c 6 \sp Ƙawaye \q1 \v 1 Ina ƙaunataccenki ya tafi, \q2 yake mafiya kyau cikin mata? \q1 Wace hanya ce ƙaunataccenki ya bi, \q2 don mu taimake ki nemansa. \sp Ƙaunatacciya \q1 \v 2 Ƙaunataccena ya gangara zuwa lambunsa, \q2 zuwa inda fangulan kayan yaji suke, \q1 don yă yi kiwo a cikin lambun \q2 don kuma yă tattara furen bi-rana. \q1 \v 3 Ni na ƙaunataccena ce, ƙaunataccena kuma nawa ne; \q2 yana kiwo a cikin furen bi-rana. \sp Ƙaunatacce \q1 \v 4 Ke kyakkyawa ce, ƙaunatacciyata, kamar Tirza, \q2 kyakkyawa kuma kamar Urushalima, \q2 mai daraja kamar mayaƙa da tutoti. \q1 \v 5 Ki kau da idanu daga gare ni; \q2 gama suna rinjayata. \q1 Gashinki yana kama da garken awakin \q2 da suke gangarawa daga Gileyad. \q1 \v 6 Haƙoranki suna kama da garken tumakin \q2 da suke haurawa daga inda aka yi musu wanka. \q1 Kowanne yana tare da ɗan’uwansa; \q2 babu waninsu da yake shi kaɗai. \q1 \v 7 Kumatunki sun yi kamar rumman \q2 da aka tsaga biyu a cikin lulluɓinki. \q1 \v 8 Sarauniyoyi sittin za su iya kasance a can, \q2 da ƙwarƙwarai tamanin \q2 da kuma budurwai da suka wuce ƙirge; \q1 \v 9 amma kurciyata, cikakkiyata, dabam take, \q2 tilo kuwa ga mahaifiyarta, \q2 ’yar lele ga wadda ta haife ta. \q1 ’Yan mata sun gan ta suka ce da ita mai albarka; \q2 sarauniyoyi da ƙwarƙwarai sun yabe ta. \sp Ƙawaye \q1 \v 10 Wace ce wannan da ta bayyana sai ka ce ketowar alfijir? \q2 Kyakkyawa kamar wata, mai haske kamar rana, \q2 mai daraja kamar taurari a jere? \sp Ƙaunatacce \q1 \v 11 Na gangara zuwa cikin itatuwan almon \q2 don in ga ƙananan itatuwan da suke girma a kwari, \q1 don in ga ko inabi sun yi ’ya’ya \q2 ko rumman suna fid da furanni. \q1 \v 12 Kafin in san wani abu, \q2 sha’awarta ta sa ni a cikin keken yaƙin sarkin mutanena.\f + \fr 6.12 \fr*\ft Ko kuwa \ft*\fqa cikin keken yaƙin Amminadab; \fqa*\ft Ko kuwa \ft*\fqa cikin keken yaƙin mutanen sarki\fqa*\f* \sp Ƙawaye \q1 \v 13 Ki dawo, ki dawo, ya Bashulammiya; \q2 ki dawo, ki dawo, don mu dube ki! \sp Ƙaunatacce \q1 Don me kuke duban Bashulammiya \q2 sai ka ce rawar Mahanayim? \b \c 7 \q1 \v 1 Ƙafafunki a cikin takalma kyakkyawa ne, \q2 Ya diyar sarki! \q1 Tsarin ƙafafunki sun yi kamar kayan ado masu daraja, \q2 aikin hannun gwanin sassaƙa. \q1 \v 2 Cibinki kamar kwaf ne \q2 da bai taɓa rasa gaurayayyen ruwan inabi ba. \q1 Kwankwasonki ya yi kamar damin alkama \q2 wanda furen bi-rana ya kewaye. \q1 \v 3 Nonanki sun yi kamar bareyi biyu, \q2 tagwayen barewa. \q1 \v 4 Wuyanki ya yi kamar hasumiyar hauren giwa. \q1 Idanunki sun yi kamar tafkin Heshbon \q2 kusa da ƙofar Bat Rabbim. \q1 Hancinki ya yi kamar hasumiyar Lebanon \q2 wadda take duban Damaskus. \q1 \v 5 Kanki ya yi miki rawani kamar Dutsen Karmel. \q2 Gashinki ya yi kamar shunayya; \q2 yakan ɗauke hankalin sarki. \q1 \v 6 Kai! Ke kyakkyawa ce kuma kina sa ni jin daɗi, \q2 Ya ƙaunatacciya, da farin cikin da kike kawo! \q1 \v 7 Tsayinki ya yi kamar itacen dabino, \q2 kuma nonanki sun yi kamar ’ya’yan itace. \q1 \v 8 Na ce, “Zan hau itacen dabino; \q2 zan kama ’ya’yansa.” \q1 Bari nonanki su zama kamar nonna kuringa, \q2 ƙanshin numfashinki ya yi kamar gawasa, \q2 \v 9 kuma bakinki ya yi kamar ruwan inabi mafi kyau. \sp Ƙaunatacciya \q1 Bari ruwan inabi yă wuce kai tsaye zuwa ga ƙaunataccena, \q2 yana gudu a hankali a leɓuna da kuma haƙora. \q1 \v 10 Ni ta ƙaunataccena ce, \q2 kuma sha’awarsa domina ne. \q1 \v 11 Ka zo, ƙaunataccena, bari mu je bayan gari, \q2 bari mu kwana a ƙauye. \q1 \v 12 Bari mu tafi gonar inabi da sassafe \q2 don mu ga ko kuringar ta yi ’ya’ya, \q1 ko furanninsu sun buɗe, \q2 ko rumman sun yi fure, \q2 a can zan nuna maka ƙaunata. \q1 \v 13 Manta-uwa sun ba da ƙanshinsu, \q2 a bakin ƙofa kuwa akwai kowane abinci mai daɗi, \q2 sabo da tsoho, \q2 da na ajiye dominka, ƙaunataccena. \b \c 8 \q1 \v 1 Da a ce kai ɗan’uwa ne gare ni, \q2 wanda nonon mahaifiyata sun shayar! \q1 Da in na same ka a waje, \q2 na sumbace ka, \q2 babu wanda zai rena ni. \q1 \v 2 Da sai in bi da kai \q2 in kawo ka gidan mahaifiyata, \q2 ita da ta koyar da ni. \q1 Da na ba ka ruwan inabi gaurayayye da kayan yaji ka sha, \q2 zaƙin rumman nawa. \q1 \v 3 Hannunsa na hagu yana a ƙarƙashin kaina, \q2 hannunsa na dama kuma ya rungume ni. \q1 \v 4 ’Yan matan Urushalima, ku yi mini alkawari. \q2 Ba za ku tā da ko ku farka ƙauna ba \q2 sai haka ya zama lalle. \sp Ƙawaye \q1 \v 5 Wace ce wannan da take haurawa daga hamada \q2 tana dogara a kan ƙaunataccenta? \sp Ƙaunatacciya \q1 A ƙarƙashin itacen gawasa na farkar da ke, \q2 a wurin da aka haife ki, \q2 wurin da mahaifiyarki ta haife ki. \q1 \v 6 Ka sa ni kamar hatimi a zuciyarka, \q2 kamar hatimi a hannunka; \q1 gama ƙauna tana da ƙarfi kamar mutuwa, \q2 kishinta yana kamar muguntar kabari, \q1 yana ƙuna kamar wuta mai ci, \q2 kamar gagarumar wuta.\f + \fr 8.6 \fr*\ft Ko kuwa \ft*\fqa / kamar harshen wutar \+nd Ubangiji\+nd*.\fqa*\f* \q1 \v 7 Ruwa da yawa ba zai iya kashe ƙauna ba, \q2 koguna ba za su iya kwashe ta ba. \q1 In wani zai bayar da \q2 dukan dukiyar gidansa don ƙauna, \q2 za a yi masa dariya ne kawai. \sp Ƙawaye \q1 \v 8 Muna da ƙanuwa, \q2 nonanta ba su riga sun yi girma ba. \q1 Me za mu yi da ƙanuwarmu \q2 a ranar da za a yi maganar sonta? \q1 \v 9 Da a ce ita katanga ce, \q2 da sai mu gina hasumiyar azurfa a kanta. \q1 Da a ce ita ƙofa ce, \q2 da sai mun yi mata ƙyauren itacen al’ul. \sp Ƙaunatacciya \q1 \v 10 Ni katanga ce \q2 kuma nonaina sun yi kamar hasumiya. \q1 Ta haka na zama idanunsa \q2 kamar wanda yake kawo gamsuwa. \q1 \v 11 Solomon ya kasance da gonar inabi a Ba’al-Hamon; \q2 ya ba da hayar gonar inabi ga ’yan haya. \q1 Kowanne zai biya shekel dubu na azurfa \q2 don ’ya’yan inabin. \q1 \v 12 Amma gonar inabina nawa ne da zan bayar; \q2 shekel dubu naka ne, ya Solomon, \q2 kuma ɗari biyu na waɗanda suke lura da ’ya’yan itatuwansa ne. \sp Ƙaunatacce \q1 \v 13 Ke da kike zaune a cikin lambu \q2 da ƙawaye suna lura da ke, \q2 bari in ji muryarki! \sp Ƙaunatacciya \q1 \v 14 Ka zo, ƙaunataccena, \q2 ka zama kamar barewa \q1 ko kuwa kamar ’yar batsiya \q2 a kan dutsen da kayan yaji suke a shimfiɗe.