\id NAM - Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ \ide UTF-8 \h Nahum \toc1 Nahum \toc2 Nahum \toc3 Nah \mt1 Nahum \c 1 \p \v 1 Jawabi game da Ninebe a littafin wahayin Nahum, mutumin Elkosh. \b \s1 Fushin \nd Ubangiji\nd* a kan Ninebe \q1 \v 2 \nd Ubangiji\nd* Allah mai kishi ne, mai sakayya kuma. \q2 \nd Ubangiji\nd* Allah mai kishi ne, mai ɗaukar fansa kuma. \q1 \nd Ubangiji\nd* yakan ɗauki fansa a kan maƙiyansa, \q2 yakan ci gaba da fushi a kan abokan gābansa. \q1 \v 3 \nd Ubangiji\nd* mai jinkirin fushi ne, mai iko duka kuma. \q2 \nd Ubangiji\nd* ba zai bar masu zunubi babu horo ba. \q1 Hanyarsa tana cikin guguwa da kuma hadari, \q2 gizagizai kuwa su ne ƙurar ƙafafunsa. \q1 \v 4 Yakan tsawata wa teku yă kuma busar da shi; \q2 yakan sa dukan koguna su kafe. \q1 Bashan da Karmel sun yi yaushi \q2 tohon Lebanon kuma ya koɗe. \q1 \v 5 Duwatsu suna rawan jiki a gabansa \q2 tuddai kuma sun narke. \q1 Duniya da dukan abin da yake cikinta \q2 suna rawan jiki a gabansa. \q1 \v 6 Wa zai iya tsaya wa fushinsa? \q2 Wa yake da ikon jimre wa zafin hasalarsa? \q1 Ana zuba fushinsa kamar wuta; \q2 aka kuma ragargaza duwatsu a gabansa. \b \q1 \v 7 \nd Ubangiji\nd* nagari ne, \q2 mafaka kuma a lokacin wahala. \q1 Yana kula da waɗanda suka dogara gare shi, \q2 \v 8 amma da ambaliyar ruwa \q1 zai kawo Ninebe ga ƙarshe; \q2 zai fafari maƙiyansa zuwa cikin duhu. \b \q1 \v 9 Dukan abin da suke ƙullawa game da \nd Ubangiji\nd*\f + \fr 1.9 \fr*\ft Ko kuwa \ft*\fqa Mene ne ku maƙiya kuke ƙullawa a kan \+nd Ubangiji\+nd*? Shi\fqa*\f* zai kawo ga ƙarshe; \q2 wahala ba za tă sāke komowa ƙaro na biyu ba. \q1 \v 10 Za su sarƙafe a ƙaya, \q2 za su kuma bugu da ruwan inabinsu; \q1 za a laƙume su kamar busasshiyar ciyawa.\f + \fr 1.10 \fr*\ft ma’anar kalman nan Ibraniyanci babu tabbas.\ft*\f* \q1 \v 11 Daga cikinki, ya Ninebe wani ya fito \q2 wanda ya ƙulla wa \nd Ubangiji\nd* makirci \q2 yana ba da mugayen shawarwari. \p \v 12 Ga abin da \nd Ubangiji\nd* ya ce, \q1 “Ko da yake sun yi tarayya, suna kuma da yawa, \q2 za a yanke su, a kawar a su. \q1 Ko da yake na ba ki azaba, ya Yahuda, \q2 ba zan ƙara ba ki azaba ba. \q1 \v 13 Yanzu zan karya karkiyarsu daga wuyanki \q2 in kuma tsittsinke sarƙar da suka ɗaura ki.” \b \q1 \v 14 \nd Ubangiji\nd* ya ba da umarni game da ke Ninebe, \q2 “Ba za ki sami zuriyar da za tă ci gaba da sunanki ba. \q1 Zan rurrushe siffofin da kuka sassaƙa da kuma gumakan da kuka ƙera \q2 gumakan da suke a cikin haikalin allolinku. \q1 Zan shirya kabarinki, \q2 domin ke muguwa ce.” \b \q1 \v 15 Duba, can a bisa duwatsu, \q2 ga ƙafafu mai kawo labari mai daɗi, \q2 wanda yake shelar salama! \q1 Ki yi bukukkuwanki, ya Yahuda, \q2 ki kuma cika wa’adodinki. \q1 Mugaye ba za su ƙara mamaye ki ba; \q2 domin za a hallaka su ƙaƙaf. \c 2 \s1 Ninebe za tă fāɗi \q1 \v 1 Mai hari yana matsowa a kanki, Ninebe. \q2 Ki tsare mafaka, \q1 ki yi gadin hanya \q2 ki sha ɗamara \q2 ki tattaro dukan ƙarfinki! \b \q1 \v 2 \nd Ubangiji\nd* zai maido da darajar Yaƙub, \q2 kamar ta Isra’ila, \q1 ko da yake masu washewa sun washe su \q2 suka kuma lalatar da inabinsu. \b \q1 \v 3 Garkuwoyin sojojinsa ja wur ne; \q2 jarumawansa suna sanye da kaya masu ruwan jan garura. \q1 Ƙarafan kekunan yaƙi suna walƙiya \q2 a ranar da aka shirya su; \q1 ana kaɗa māsu da bantsoro.\f + \fr 2.3 \fr*\ft Da Ibraniyanci; Seftuwajin da Siriyak / \ft*\fqa mahayan dawakai suna kai da kawowa\fqa*\f* \q1 \v 4 Kekunan yaƙi sun zabura a tituna, \q2 suna kai da kawowa a dandali. \q1 Suna walƙiya kamar tocila \q2 suna sheƙawa a guje kamar walƙiya. \b \q1 \v 5 Ninebe ta tattara rundunarta, \q2 duk da haka sun yi ta tuntuɓe a kan hanyarsu. \q1 Sun ruga zuwa katangan birnin, \q2 sun sanya garkuwar kāriya a inda ya kamata. \q1 \v 6 An buɗe ƙofofin rafuffukan \q2 sai wurin ya rurrushe. \q1 \v 7 An umarta\f + \fr 2.7 \fr*\ft Ma’anar kalmar da Ibraniyanci babu tabbas.\ft*\f* cewa birnin \q2 za tă tafi bauta, za a kuma yi gaba da su. \q1 Bayi ’yan mata suna kuka kamar tattabaru \q2 suna buga ƙirjinsu. \q1 \v 8 Ninebe tana kama da tafki, \q2 wanda ruwanta yana yoyo. \q1 Suna kuka suna cewa, “Ku tsaya! Ku tsaya,” \q2 amma ba wanda ya waiga. \q1 \v 9 A washe azurfa; \q2 a washe zinariya; \q1 dukiyarsu ba ta da iyaka, \q2 arzikinsu kuma ba ya ƙarewa. \q1 \v 10 Ta zama wofi, an washe ta, an tuɓe ta! \q2 Zukata sun narke, gwiwoyi suna kaɗuwa, \q2 jikuna suna rawa, fuskoki duk sun kwantsare! \b \q1 \v 11 Ina kogon zakokin nan yake yanzu, \q2 inda suka ciyar da ’ya’yansu, \q1 inda zaki da zakanya sukan shiga, \q2 da ’ya’yansu, ba mai damunsu \q1 \v 12 Zaki ya kashe abin da ya ishe ’ya’yansa \q2 ya kuma murɗe wuyan dabbobi \q1 ya cika wurin zamansa da abin da ya kama \q2 ya cika kogwanninsa da abin da ya kashe. \b \q1 \v 13 “Ina gāba da ke,” \q2 in ji \nd Ubangiji\nd* Maɗaukaki. \q1 “Zan ƙone kekunan yaƙinki, \q2 takobi kuma zai fafare ’ya’yan zakokinki. \q2 Ba kuma zan bar miki namun jejin da za ki kashe a duniya ba. \q1 Ba kuwa za a ƙara jin \q2 muryar ’yan saƙonki ba.” \c 3 \s1 Kaiton Ninebe \q1 \v 1 Kaiton birni mai zub da jini, \q2 wadda take cike da ƙarairayi, \q1 cike da ganima, \q2 wadda ba a rasa masu fāɗawa cikin wahala! \q1 \v 2 Ku ji karar bulala \q2 da kwaramniyar ƙafafu, \q1 da sukuwar dawakai \q2 da girgizar kekunan yaƙi! \q1 \v 3 Mahaya dawakai sun kunno kai, \q2 takuba suna walƙiya, \q2 māsu kuma suna ƙyali; \q1 ga ɗumbun da aka kashe \q2 ga tsibin matattu, \q1 gawawwaki ba iyaka, \q2 mutane suna tuntuɓe da gawawwaki, \q1 \v 4 duk saboda yawan sha’awace-sha’awacen karuwa, \q2 mai daɗin baki, uwargidan maita, \q1 wadda ta ɓad da al’ummai ta wurin karuwancinta \q2 ta kuma ɓad da mutane ta wurin maitancinta. \b \q1 \v 5 “Ina gāba da ke,” in ji \nd Ubangiji\nd* Maɗaukaki. \q2 “Zan kware fatarinki a idonki. \q1 Zan nuna wa al’ummai tsiraicinki, \q2 masarautai kuma kunyarki. \q1 \v 6 Zan watsa miki ƙazanta, \q2 in yi miki wulaƙanci \q2 in kuma mai da ke abin reni. \q1 \v 7 Duk wanda ya gan ki zai gudu daga gare ki yana cewa, \q2 ‘Ninebe ta lalace, wa zai yi makoki domin ta?’ \q2 Ina zan sami wani wanda zai yi miki ta’aziyya?” \b \q1 \v 8 Kin fi Tebes\f + \fr 3.8 \fr*\ft Ibraniyanci \ft*\fqa Ba Amon\fqa*\f* ne \q2 da take a bakin Nilu, \q2 da ruwa yake kewaye da ita? \q1 Rafi shi ne kāriyarta, \q2 ruwanta kuma katanga. \q1 \v 9 Kush\f + \fr 3.9 \fr*\ft Wato, yankin Nilu na Bisa\ft*\f* da kuma Masar su ne ƙarfinta marar iyaka; \q2 Fut da Libiya suna cikin mataimakanta. \q1 \v 10 Duk da haka an tafi da ita \q2 ta kuma tafi bauta. \q1 Aka fyaɗa ƙanananta da ƙasa \q2 aka yayyanka su gunduwa-gunduwa a kan kowane titi. \q1 Aka jefa ƙuri’a a kan manyan mutanenta, \q2 aka daure manyan mutanenta da sarƙoƙi. \q1 \v 11 Ke ma za ki bugu, \q2 za ki ɓuya. \q2 Ki kuma nemi mafaka daga wurin abokin gāba. \b \q1 \v 12 Dukan kagarunki suna kama da itatuwan ɓaure \q2 da ’ya’yansu da suka nuna. \q1 Da an girgiza, \q2 sai ɓaure su zuba a bakin mai sha. \q1 \v 13 Dubi mayaƙanki, \q2 duk mata ne! \q1 Ƙofofin ƙasarki \q2 a buɗe suke ga abokan gābanki, \q2 wuta ta cinye madogaransu. \b \q1 \v 14 Ki ja ruwa gama za a kewaye ki da yaƙi. \q2 Ki ƙara ƙarfin kagaranki! \q2 Ki kwaɓa laka, \q2 ki sassaƙa turmi \q2 ki gyara abin yin tubali! \q1 \v 15 A can wuta za tă cinye ki; \q2 takobi zai sare ki, \q2 kuma kamar fāra, za a cinye ki. \q1 Ki riɓaɓɓanya kamar fāra, \q2 ki riɓaɓɓanya kamar fārin ɗango! \q1 \v 16 Kin ƙara yawan masu kasuwancinki \q2 har sai da suka fi taurarin sama. \q1 Amma kamar fāra sun cinye ƙasar \q2 sa’an nan suka tashi, suka tafi. \q1 \v 17 Masu tsaronki suna kama da fāri ɗango, \q2 shugabanninki sun yi cincirindo kamar fārin ɗango \q1 da suka sauka a kan bango a rana mai sanyi, \q2 amma da rana ta fito, duk za su tashi su tafi, \q2 ba kuma wanda ya san inda suka nufa. \b \q1 \v 18 Ya sarkin Assuriya, makiyayanka\f + \fr 3.18 \fr*\ft Ko kuwa \ft*\fqa masu mulki\fqa*\f* sun yi barci; \q2 manyan mutanenka sun kwanta su huta. \q1 An watsar da mutanenka a cikin duwatsu, \q2 ba wanda zai tattaro su. \q1 \v 19 Ba abin da zai warkar da rauninka; \q2 rauninka ya yi muni. \q1 Duk wanda ya ji labarinka \q2 zai tafa hannuwansa saboda farin cikin fāɗuwarka, \q1 gama wane ne bai ji \q2 jiki a hannunka ba?