\id MAL - Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ \ide UTF-8 \h Malaki \toc1 Malaki \toc2 Malaki \toc3 Mal \mt1 Malaki \c 1 \p \v 1 Annabci, wannan ita ce maganar \nd Ubangiji\nd* ga Isra’ila ta wurin Malaki.\f + \fr 1.1 \fr*\fq Malaki \fq*\ft yana nufin \ft*\fqa manzona.\fqa*\f* \s1 An ƙaunaci Yaƙub, aka ƙi Isuwa \p \v 2 “Na ƙaunace ku, in ji \nd Ubangiji\nd*. \p “Amma sai kuka ce, ‘Yaya ka ƙaunace mu?’ \p “Isuwa ba ɗan’uwan Yaƙub ba ne?” In ji \nd Ubangiji\nd*. “Duk da haka na ƙaunaci Yaƙub, \v 3 amma na ƙi Isuwa, na kuma mai da ƙasarsa da take kan duwatsu kango, na ba da gādonsa ga dilolin hamada.” \p \v 4 Edom zai iya cewa, “Ko da yake an ragargaza mu, ai, za mu sāke gina kufanmu.” \p Amma ga abin da \nd Ubangiji\nd* Maɗaukaki ya ce, “Za su iya gini, amma zan rushe. Za a ce da su Muguwar Ƙasa, mutane da kullum suke a ƙarƙashi fushin \nd Ubangiji\nd*. \v 5 Za ku ga wannan da idanunku ku kuma ce, ‘\nd Ubangiji\nd* da girma yake, har gaba da iyakokin Isra’ila ma!’ \s1 Hadayu masu aibi \p \v 6 “Ɗa yakan girmama mahaifinsa, bawa kuma yakan girmama maigidansa. In ni mahaifi ne, ina girman da ya dace da ni? In ni maigida ne, ina girman da ya dace da ni?” In ji \nd Ubangiji\nd* Maɗaukaki. \p “Ku firistoci, ku ne kuka rena sunana. \p “Amma sai kuka ce, ‘Yaya muka rena sunanka?’ \p \v 7 “Kun ajiye abinci mai ƙazanta a kan bagadena. \p “Sai kuka ce, ‘Yaya muka ƙazantar da kai?’ \p “Ta wurin cewa teburin \nd Ubangiji\nd* abin reni ne. \v 8 Sa’ad da kuka kawo makauniyar dabba don ku miƙa mini hadaya, wannan daidai ne? Sa’ad da kuka miƙa gurguwar dabba ko marar lafiya, wannan daidai ne? Ku gwada ba wa gwamnanku irin wannan ku gani! Kuna gani zai ji daɗinku? Zai karɓe ku ne?” In ji \nd Ubangiji\nd* Maɗaukaki. \p \v 9 “To, firistoci yanzu ku gwada ku roƙi Allah yă yi mana alheri. Da irin hadayun nan a hannuwanku ne zai ji ku?” In ji \nd Ubangiji\nd* Maɗaukaki. \p \v 10 “Kash, da ma wani daga cikinku ya rufe ƙofofin haikali don kada ku shiga, ku hura wuta marar amfani a bisa bagadena! Ba na jin daɗinku, ba zan kuwa karɓi hadaya daga hannuwanku ba” in ji \nd Ubangiji\nd* Maɗaukaki. \v 11 Sunana zai zama mai girma a cikin al’ummai, daga fitowar rana har zuwa fāɗuwarta. A kowane wuri za a miƙa wa sunana turare da tsabtacciyar hadaya domin sunana zai zama mai girma a cikin al’ummai, in ji \nd Ubangiji\nd* Maɗaukaki. \p \v 12 “Amma kun ƙazantar da sunana ta wurin cewa ‘Teburin Ubangiji ya ƙazantu,’ kuka kuma yi magana a kan abincinsa kuna cewa, ‘Abin reni ne.’ \v 13 Kun kuma ce, ‘Mun gaji da irin wannan wahala!’ Kuna hura mini hancin reni,” in ji \nd Ubangiji\nd* Maɗaukaki. \p “Sa’ad da kuka kawo raunannu, gurguntattun dabbobi, ko kuma dabbobi masu fama da cuta, kuka kuma miƙa su hadaya, kuna gani zan karɓi wannan daga gare ku?” In ji \nd Ubangiji\nd*. \v 14 “La’ananne ne macucin da yake da lafiyayyiyar dabba namiji a garkensa wadda ya yi alkawari zai bayar, amma sai ya miƙa hadayar dabba mai aibi ga Ubangiji. Gama ni babban sarki ne, za a kuma ji tsoron sunana a cikin al’ummai,” in ji \nd Ubangiji\nd* Maɗaukaki. \c 2 \s1 Ƙarin gargaɗi ga firistoci \p \v 1 “Yanzu fa wannan gargaɗi dominku ne, ku firistoci. \v 2 In ba ku saurara ba, in kuma ba ku sa zuciyarku ga girmama sunana ba, zan aukar muku da la’ana, zan kuma la’antar da albarkunku. I, na riga na la’anta su, domin ba ku sa zuciyarku ga girmama ni ba, in ji \nd Ubangiji\nd* Maɗaukaki. \p \v 3 “Saboda ku zan tsawata\f + \fr 2.3 \fr*\ft Ko kuwa \ft*\fqa yanke \fqa*\ft (dubi Seftuwajin)\ft*\f* wa zuriyarku;\f + \fr 2.3 \fr*\ft Ko kuwa \ft*\fqa za su lalace hatsi\fqa*\f* zan watsa kashin dabbobin hadayunku a fuskokinku, a kuma kwashe ku tare da shi. \v 4 Za ku kuwa san cewa ni ne na aika muku da wannan gargaɗi domin alkawarina da Lawi yă ci gaba,” in ji \nd Ubangiji\nd* Maɗaukaki. \v 5 “Alkawarina da shi, alkawari ne na rai da salama, wanda na ba shi; domin yă girmama ni, ya kuwa girmama ni, ya kuma ji tsoron sunana ƙwarai. \v 6 Umarnin gaskiya yana a bakinsa, ba a kuma sami wani ƙarya a leɓunansa ba. Ya yi tafiya tare da ni cikin salama da adalci, ya kuwa juyo da mutane masu yawa daga zunubi. \p \v 7 “Gama ya kamata leɓunan firist su kiyaye ilimi, ya kamata kuma mutane su nemi umarni daga bakinsa, domin shi ne manzon \nd Ubangiji\nd* Maɗaukaki. \v 8 Amma sai kuka kauce hanya, ta wurin koyarwarku kuma kuka sa mutane da yawa suka yi tuntuɓe; kun keta alkawarin da na yi da Lawi,” in ji \nd Ubangiji\nd* Maɗaukaki. \v 9 “Saboda haka na sa a rena ku, a kuma wulaƙanta ku a gaban dukan mutane, domin ba ku bi hanyoyina ba amma kuka nuna sonkai a al’amuran shari’a.” \s1 Keta alkawari ta wurin kisan aure \p \v 10 Ashe, ba Mahaifi guda dukanmu muke da shi ba? Ba Allah ɗaya ne ya halicce mu ba? Don me muka keta alkawarin kakanninmu ta wurin cin amanar juna? \p \v 11 Yahuda ya ci amana. An yi abin kunya a Isra’ila da kuma a Urushalima. Yahuda ya ƙazantar da wuri mai tsarkin da \nd Ubangiji\nd* yake ƙauna, ta wurin auren ’yar wani baƙon allah. \v 12 Game da mutumin da ya aikata wannan, ko wane ne shi, bari \nd Ubangiji\nd* yă yanke shi daga tentunan Yaƙub,\f + \fr 2.12 \fr*\ft Ko kuwa \ft*\fv 12 \fv*\fqa Bari \+nd Ubangiji\+nd* yă yanke daga tentunan Yaƙub duk wanda ya ba da shaida a madadin mutumin da ya aikata wannan\fqa*\f* ko da ma ya kawo hadayu ga \nd Ubangiji\nd* Maɗaukaki. \p \v 13 Ga kuma wani abin da kuke yi. Kukan cika bagaden \nd Ubangiji\nd* da hawaye. Kukan yi kuka kuna ihu gama \nd Ubangiji\nd* ba ya mai da hankali ga hadayunku ko yă karɓe su da farin ciki. \v 14 Kukan ce, “Don me ba ya karɓan hadayunmu?” Ai, domin \nd Ubangiji\nd* ya zama shaida tsakaninka da matar ƙuruciyarka, gama ka keta amanar da ka yi mata, ko da yake ita abokiyar zamanka ce, matar aurenka ta alkawari. \p \v 15 Ashe, \nd Ubangiji\nd* bai maishe su ɗaya ba? Cikin jiki da ruhu, su nasa ne. Me ya sa suke ɗaya? Domin yana neman ’ya’ya masu tsoron Allah.\f + \fr 2.15 \fr*\ft Ko kuwa \ft*\fv 15 \fv*\fqa Amma wanda yake mahaifinmu bai yi haka ba, muddin yana da rai. Me yake nema? Zuriya daga Allah\fqa*\f* Saboda haka sai ka lura da kanka, kada kuma ka ci amanar matar ƙuruciyarka. \p \v 16 “Na ƙi kisan aure,” in ji \nd Ubangiji\nd*, Allah na Isra’ila. “Na kuma ƙi mutumin da ya rufe kansa da tashin hankali kamar riga,” in ji \nd Ubangiji\nd* Maɗaukaki. \p Saboda haka sai ka lura da kanka, kada kuma ka ci amana. \s1 Ranar shari’a \p \v 17 Kun sa \nd Ubangiji\nd* Maɗaukaki ya gaji da maganganunku. \p Sai kuka ce, “Yaya muka sa ya gaji?” \p Kun yi haka ta wurin cewa, “Duk waɗanda suke aikata mugunta, mutanen kirki ne a gaban \nd Ubangiji\nd*, yana kuwa jin daɗinsu,” kuna kuma cewa, “Ina Allah mai adalci yake?” \c 3 \p \v 1 “Duba, zan aika manzona, wanda zai shirya hanya a gabana. Sa’an nan a farat ɗaya \nd Ubangiji\nd* wanda kuke nema zai zo haikalinsa. Manzon alkawari, wanda kuke sa zuciya kuwa zai zo,” in ji \nd Ubangiji\nd* Maɗaukaki. \p \v 2 Amma wa zai jure wa ranar zuwansa? Wa zai iya tsaya sa’ad da ya bayyana? Gama zai zama kamar wuta mai tace ƙarfe, ko sabulu mai wanki. \v 3 Zai zama kamar mai tace azurfa da mai tsarkaketa; zai tsabtacce Lawiyawa, yă kuma tace su kamar zinariya da azurfa. Sa’an nan \nd Ubangiji\nd* zai sami mutanen da za su kawo hadayu a cikin adalci. \v 4 Hadayun Yahuda da na Urushalima za su zama yardajje ga \nd Ubangiji\nd*, za su zama kamar a kwanakin da suka wuce, kamar a shekarun baya. \p \v 5 “Ta haka zan zo kusa da ku don in yi hukunci. Zan hanzarta ba da shaida a kan masu yin sihiri, da mazinata da masu shaidar zur. Zan ba da shaida a kan waɗanda suke zaluntar ma’aikata a kan albashinsu, da waɗanda suke ƙwarar gwauraye da marayu, suna kuma hana baƙi samun adalci, ba sa ma tsorona,” in ji \nd Ubangiji\nd* Maɗaukaki. \s1 Keta alkawari ta wurin ƙin fid da zakka \p \v 6 “Ni \nd Ubangiji\nd* ba na canjawa. Shi ya sa ku zuriyar Yaƙub, ba a hallaka ku ƙaƙaf ba. \v 7 Tun zamanin kakanninku, kun juye wa ƙa’idodina baya, ba ku kuma kiyaye su ba. Ku komo gare ni, ni kuma zan koma gare ku,” in ji \nd Ubangiji\nd* Maɗaukaki. \p “Amma sai kuka ce, ‘Yaya za mu koma gare ka?’ \p \v 8 “Mutum zai iya yi wa Allah fashi ne? Duk da haka kun yi mini fashi. \p “Amma sai kuka ce, ‘Yaya muka yi maka fashi?’ \p “A wajen zakka da hadayu. \v 9 Kuna ƙarƙashin la’ana, dukan al’ummarku, domin kuna yin mini fashi. \v 10 Ku kawo dukan zakka cikin gidan ajiya, don a kasance da abinci a gidana. Ku gwada ni a wannan ku ga, ko ba zan buɗe taskokin sama in zubo muku albarka mai yawa, wadda har ba za ku rasa wurin sa ta ba, in ji \nd Ubangiji\nd* Maɗaukaki. \v 11 Zan hana ƙwari su cinye hatsinku. Kuringar inabi a gonakinku kuma ba za su zubar da ’ya’yansu kafin su nuna ba,” in ji \nd Ubangiji\nd* Maɗaukaki. \v 12 “Sa’an nan dukan al’ummai za su ce da ku masu albarka, gama ƙasarku za tă yi daɗin zama,” in ji \nd Ubangiji\nd* Maɗaukaki. \p \v 13 “Kun faɗi mugayen abubuwa a kaina,” in ji \nd Ubangiji\nd*. \p “Duk da haka kuka ce, ‘Me muka faɗa a kanka?’ \p \v 14 “Kun ce, ‘Ba amfani a bauta wa Allah. Wanda amfani muka samu ta wurin kiyaye umarnansa muna yawo kamar masu makoki a gaban \nd Ubangiji\nd* Maɗaukaki? \v 15 A ganinmu, masu girman kai suna jin daɗi. Masu aikata mugunta kuwa ba arziki kaɗai suka yi ba, amma sukan gwada Allah da mugayen ayyukansu, su kuwa zauna lafiya.’ ” \p \v 16 Sa’an nan waɗanda suke tsoron \nd Ubangiji\nd* suka yi magana da juna, \nd Ubangiji\nd* kuwa ya kasa kunne ya kuma ji. A gabansa aka rubuta a littafin tarihi waɗanda suke tsoron \nd Ubangiji\nd*, suna kuma girmama sunansa. \p \v 17 “A ranar da na shirya ajiyayyen mallakata\f + \fr 3.17 \fr*\ft Ko kuwa \ft*\fqa Maɗaukaki, “ajiyayyen mallakata, a ranar da na aikata”\fqa*\f*, za su zama nawa,” in ji \nd Ubangiji\nd* Maɗaukaki. “Zan ji kansu kamar yadda mahaifi cikin tausayi yakan ji kan ɗansa wanda yake masa hidima. \v 18 Za ku kuma ga bambanci tsakanin masu adalci da mugaye, tsakanin waɗanda suke wa Allah hidima da kuma waɗanda ba sa yi. \c 4 \s1 Ranar \nd Ubangiji\nd* \p \v 1 “Tabbatacce rana tana zuwa; za tă yi ƙuna kamar wutar maƙera. Dukan masu girman kai da kowane mai aikata mugunta zai zama ciyawa, wannan rana mai zuwa za tă ƙone su. Babu saiwa ko reshen da za a bar musu,” in ji \nd Ubangiji\nd* Maɗaukaki. \v 2 Amma ku da kuke girmama sunana, ranar adalci za tă fito tare da warkarwa a fikafikanta. Za ku kuwa fita kuna tsalle kamar ’yan maruƙan da aka sake daga garke. \v 3 Sa’an nan za ku tattake mugaye; za su zama toka a ƙarƙashin tafin ƙafafunku a ranar da zan aikata waɗannan abubuwa, in ji \nd Ubangiji\nd* Maɗaukaki. \p \v 4 “Ku tuna da dokar bawana Musa, ƙa’idodi da dokokin da na ba shi a Horeb domin dukan Isra’ila. \p \v 5 “Ga shi, zan aika muku da annabi Iliya kafin babbar ranan nan mai banrazana ta \nd Ubangiji\nd* tă zo. \v 6 Zai juye zukatan iyaye ga ’ya’yansu, zukatan ’ya’ya kuma ga iyayensu; in ba haka ba zan bugi ƙasar da hallaka gaba ɗaya.”