\id JOL - Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ \ide UTF-8 \h Yowel \toc1 Yowel \toc2 Yowel \toc3 Yow \mt1 Yowel \c 1 \p \v 1 Maganar \nd Ubangiji\nd* wadda ta zo wurin Yowel ɗan Fetuwel. \b \s1 Mamayar da fāra ta yi \q1 \v 2 Ku ji wannan, ku dattawa, \q2 ku kasa kunne, dukan waɗanda suke zaune a ƙasar. \q1 Ko wani abu makamancin haka ya taɓa faruwa a kwanakinku \q2 ko a kwanakin kakanninku? \q1 \v 3 Ku faɗa wa ’ya’yanku, \q2 bari kuma ’ya’yanku su faɗa wa ’ya’yansu, \q2 ’ya’yansu kuma su faɗa wa tsara ta gaba. \q1 \v 4 Abin da ɗango ya bari \q2 fāri masu girma sun cinye; \q1 abin da fāri masu girma suka bari, \q2 burduduwa ta cinye; \q1 abin da burduduwa ta bari sauran kwari\f + \fr 1.4 \fr*\ft A nan ma’anar kalmomin nan huɗu na Ibraniyanci da aka yi amfani da su da yake nuna fāra ba a san tabbatacciyar ma’anar ba.\ft*\f* sun cinye. \b \q1 \v 5 Ku farka, ku bugaggu, ku yi kuka! \q2 Ku yi kuka da ƙarfi, ku dukan mashayan ruwan inabi; \q1 ku yi kuka mai ƙarfi saboda sabon ruwan inabi, \q2 gama an riga an ƙwace ta daga leɓunanku. \q1 \v 6 Wata al’umma ta mamaye ƙasata, \q2 tana da ƙarfi ba ta kuma ƙidayuwa; \q1 tana da haƙoran zaki, \q2 da zagar zakanya. \q1 \v 7 Ta mayar da kuringar inabina kango \q2 ta kuma lalatar da itatuwan ɓaurena. \q1 Ta ɓamɓare bayansu duka \q2 ta kuma jefar da su \q2 ta bar rassansu fari fat. \b \q1 \v 8 Ku yi makoki kamar budurwa\f + \fr 1.8 \fr*\ft Ko kuwa \ft*\fqa yarinya\fqa*\f* \q2 a cikin tsummoki \q1 tana baƙin ciki domin mijinta\f + \fr 1.8 \fr*\ft Ko kuwa \ft*\fqa wanda suka yi alkawarin aure\fqa*\f* na ƙuruciyarta. \q1 \v 9 Hadayun hatsi da hadayun sha \q2 an yanke su daga gidan \nd Ubangiji\nd*. \q1 Firistoci suna makoki, \q2 su waɗanda suke yi wa \nd Ubangiji\nd* hidima. \q1 \v 10 Filaye sun zama marasa amfani, \q2 ƙasa ta bushe;\f + \fr 1.10 \fr*\ft Ko kuwa \ft*\fqa ƙasa tana makoki\fqa*\f* \q1 an lalatar da hatsi, \q2 sabon ruwan inabin ya bushe, \q2 mai kuma ba amfani. \b \q1 \v 11 Ku fid da zuciya, ku manoma, \q2 ku yi ihu, ku masu noma inabi; \q1 ku yi baƙin ciki saboda alkama da sha’ir, \q2 saboda an lalata girbin filaye. \q1 \v 12 Kuringar inabin ta bushe \q2 itacen ɓaure kuma ya yi yaushi, \q1 ’ya’yan rumman, itacen dabino da itacen gawasa, \q2 dukan itatuwan filaye, sun bushe. \q1 Tabbatacce farin cikin ’yan adam \q2 ya bushe. \s1 Kira don makoki \q1 \v 13 Ku sa tsummoki, ya firistoci, ku yi makoki; \q2 ku yi ihu, ku da kuke yin hidima a gaban bagade. \q1 Zo, ku kwana saye da tsummoki, \q2 ku waɗanda kuke yi wa Allahna hidima, \q1 gama an yanke hadayun hatsi da hadayun sha \q2 daga gidan Allahnku. \q1 \v 14 Ku yi shelar azumi mai tsarki; \q2 ku kira tsarkakan taro. \q1 Ku kira dattawa \q2 da kuma dukan mazaunan ƙasar \q1 zuwa gidan \nd Ubangiji\nd* Allahnku, \q2 ku kuma yi kuka ga \nd Ubangiji\nd*. \b \q1 \v 15 Kaito saboda wannan rana! \q2 Gama ranar \nd Ubangiji\nd* ta kusa, \q1 za tă zo kamar hallaka daga wurin Maɗaukaki.\f + \fr 1.15 \fr*\ft Da Ibraniyanci \ft*\fqa Shaddai\fqa*\f* \b \q1 \v 16 Ba a yanke abinci \q2 a idanunmu, \q1 farin ciki da kuma murna \q2 daga gidan Allahnmu ba? \q1 \v 17 Iri suna ta yanƙwanewa \q2 a busasshiyar ƙasa\f + \fr 1.17 \fr*\ft ma’anar wannan kalma da Ibraniyanci ba ta da tabbas.\ft*\f* \q1 Ɗakunan ajiya sun lalace, \q2 an rurrushe rumbunan hatsin, \q2 gama hatsi ya ƙare. \q1 \v 18 Ji yadda dabbobi suke nishi! \q2 Garkunan shanu sun ruɗe \q1 saboda ba su da ciyawa, \q2 har garkunan tumaki ma suna shan wahala. \b \q1 \v 19 A gare ka, ya \nd Ubangiji\nd*, nake kira, \q2 gama wuta ta cinye wurin kiwo \q1 harshen wuta kuma ya ƙone dukan itatuwan jeji. \q1 \v 20 Har ma namun jeji suna haki gare ka; \q2 rafuffuka sun bushe \q2 wuta kuma ta cinye wurin kiwo a jeji. \c 2 \s1 Rundunar fāra \q1 \v 1 Ku busa ƙaho a cikin Sihiyona; \q2 ku yi karar amo a tsaunina mai tsarki. \b \q1 Bari dukan mazaunan ƙasar su yi rawan jiki, \q2 gama ranar \nd Ubangiji\nd* tana zuwa. \q2 Tana gab da faruwa \q1 \v 2 rana ce ta baƙin duhu ƙirin, \q2 ranar gizagizai ce baƙi ƙirin. \q1 Babbar rundunar mayaƙa mai ƙarfi tana zuwa \q2 kamar ketowar alfijir a kan duwatsu \q1 yadda ba a taɓa ganin irinta ba, \q2 ba kuwa za a ƙara ganin irinta ba har tsararraki masu zuwa. \b \q1 \v 3 A gabansu wuta tana ci, \q2 a bayansu ga harshen wuta yana ci, \q1 A gabansu ƙasa ta yi kamar gonar Eden, \q2 a bayansu kuma jeji ne wofi, \q2 babu abin da ya kuɓuce musu. \q1 \v 4 Suna da kamannin dawakai; \q2 suna gudu kamar dokin yaƙi. \q1 \v 5 Da motsi kamar na kekunan yaƙi \q2 sun tsallake ƙwanƙolin duwatsu, \q1 kamar ƙarar harshen wuta mai cin tattaka, \q2 kamar runduna mai ƙarfi wadda ta ja dāgār yaƙi. \b \q1 \v 6 Da ganinsu, al’ummai sun kamu da azaba; \q2 kowace fuska ta yanƙwane. \q1 \v 7 Sukan auka kamar jarumawa; \q2 sukan hau katanga kamar sojoji. \q1 Kowa yana takawa bisa ga tsari, \q2 ba mai kaucewa. \q1 \v 8 Ba sa turin juna, \q2 kowane yakan miƙe gaba. \q1 Sukan kutsa cikin abokan gāba \q2 ba mai tsai da su. \q1 \v 9 Sukan ruga cikin birni, \q2 suna gudu a kan katanga. \q1 Sukan hau gidaje, \q2 sukan shiga ta tagogi kamar ɓarayi. \b \q1 \v 10 A gabansu duniya takan girgiza, \q2 sararin sama kuma yakan jijjigu, \q1 rana da wata su yi duhu, \q2 taurari kuma ba sa ba da haske. \q1 \v 11 \nd Ubangiji\nd* ya yi tsawa \q2 wa shugaban mayaƙansa; \q1 sojojinsa sun fi a ƙirge \q2 masu ƙarfi ne kuma su waɗanda suke biyayya da umarninsa. \q1 Ranar \nd Ubangiji\nd* da girma take; \q1 mai banrazana. \q2 Wa zai iya jure mata? \s1 Ku kyakkece zuciyarku \q1 \v 12 “Ko yanzu”, in ji \nd Ubangiji\nd*, \q2 “Ku juyo gare ni da dukan zuciyarku, \q2 da azumi da kuka da makoki.” \b \q1 \v 13 Ku kyakkece zuciyarku \q2 ba rigunanku ba. \q1 Ku juyo ga \nd Ubangiji\nd* Allahnku, \q2 gama shi mai alheri ne mai tausayi kuma \q1 mai jinkirin fushi da yawan ƙauna, \q2 yakan kuma janye daga aika da bala’i. \q1 \v 14 Wa ya sani? Ko zai juya yă kuma ji tausayi \q2 yă sa mana albarka \q1 ta wurin hadaya ta gari da hadaya ta sha \q2 wa \nd Ubangiji\nd* Allahnku. \b \q1 \v 15 A busa ƙaho a Sihiyona, \q2 a yi shelar azumi mai tsarki, \q2 a kira tsarkakan taro. \q1 \v 16 A tattara mutane; \q2 ku tsarkake taron; \q1 ku kawo dattawa wuri ɗaya; \q2 ku kuma tara yara, \q2 da waɗanda suke shan mama. \q1 Bari ango yă bar ɗakinsa \q2 amarya kuma lolokinta. \q1 \v 17 Bari firistocin da suke yin hidima a gaban \nd Ubangiji\nd*, \q2 su yi kuka tsakanin filin haikali da bagade. \q1 Bari su ce, “Ka cece mutanenka, ya \nd Ubangiji\nd*. \q2 Kada ka bar gādonka yă zama abin dariya, \q2 da abin ba’a a cikin al’ummai. \q1 Me zai sa a ce a cikin mutane, ‘Ina Allahnsu yake?’ ” \s1 Amsar \nd Ubangiji\nd* \q1 \v 18 Ta haka \nd Ubangiji\nd* zai yi kishin ƙasarsa \q2 yă kuma ji tausayin mutanensa. \p \v 19 \nd Ubangiji\nd* zai amsa\f + \fr 2.18,19 \fr*\ft Ko kuwa \ft*\fqa \+nd Ubangiji\+nd* yă ji kishin / da kuma tausayawa / \fqa*\fv 19 \fv*\fqa \+nd Ubangiji\+nd* ya amsa\fqa*\f* musu ya ce, \q1 “Ina aika da hatsi, sabon ruwan inabi, da mai, \q2 isashe da zai ƙosar da ku sosai; \q1 ba kuma zan ƙara maishe ku \q2 abin dariya ga al’ummai ba. \b \q1 \v 20 “Zan kori sojojin arewa nesa da ku, \q2 in tura su cikin busasshiyar ƙasa marar amfani kuma, \q1 kuma da sawunsu na gaba zan tura su zuwa gabashin teku\f + \fr 2.20 \fr*\ft Wato, Mediterraniyan.\ft*\f* \q2 da kuma sawunsu na baya tura su zuwa yammanci a Bahar Rum.\f + \fr 2.20 \fr*\ft wannan teku na Bahar Maliya ne\ft*\f* \q1 Warinsu kuma zai bazu; \q2 ɗoyinsu zai tashi.” \b \q1 Tabbatacce ya yi al’amura masu girma.\f + \fr 2.20 \fr*\ft Ko kuwa \ft*\fqa ya tashi. Tabbatacce ya yi abubuwa masu girma\fqa*\f* \q2 \v 21 Kada ki ji tsoro, ya ƙasa; \q2 ki yi murna ki kuma yi farin ciki. \q1 Tabbatacce \nd Ubangiji\nd* ya yi abubuwa masu girma. \q2 \v 22 Kada ku ji tsoro, ya ku namun jeji, \q2 gama wuraren kiwo sun yi kore shar. \q1 Itatuwa suna ba da ’ya’yansu; \q2 itacen ɓaure da na inabi suna ba da amfaninsu. \q1 \v 23 Ku yi murna, ya ku mutanen Sihiyona, \q2 ku yi farin ciki cikin \nd Ubangiji\nd* Allahnku, \q1 gama ya ba ku \q2 ruwan bazara cikin adalci.\f + \fr 2.23 \fr*\ft ko / \ft*\fqa mai koyar da gaskiya\fqa*\f* \q1 Yakan aika muku yayyafi a yalwace, \q2 na bazara da na kaka, kamar dā. \q1 \v 24 Masussukai za su cika da hatsi; \q2 randuna za su cika da sabon ruwan inabi da mai suna zuba. \b \q1 \v 25 “Zan mayar muku da abin da fāra suka ci a waɗannan shekaru \q2 waɗanda ɗango da fāra masu gaigayewa, \q2 da kuma sauran fāra da tarin fāra\f + \fr 2.25 \fr*\ft Takamamme ma’anar kalmomin nan guda huɗu na Ibraniyancin da aka yi amfani da su a nan domin fāra babu wanda ya sani.\ft*\f* \q1 babban mayaƙan da na aika don su fāɗa muku. \q1 \v 26 Za ku sami a wadace ku ci, har sai kun ƙoshi, \q2 za ku kuma yabi sunan \nd Ubangiji\nd* Allahnku, \q2 wanda ya yi muku ayyukan banmamaki; \q2 mutanena ba za su ƙara shan kunya ba. \q1 \v 27 Sa’an nan za ku sani ina cikin Isra’ila, \q2 cewa ni ne \nd Ubangiji\nd* Allahnku, \q2 babu wani kuma; \q1 mutanena ba za su ƙara shan kunya ba. \s1 Ranar \nd Ubangiji\nd* \q1 \v 28 “Daga baya kuma, \q2 zan zuba Ruhuna a bisan dukan mutane. \q1 ’Ya’yanku maza da mata za su yi annabci, \q2 tsofaffinku za su yi mafarkai, \q2 matasanku za su ga wahayoyi. \q1 \v 29 Har ma a bisan bayina, maza da mata, \q2 zan zuba Ruhuna a kwanakin nan. \q1 \v 30 Zan nuna abubuwan banmamaki a cikin sammai \q2 da kuma a kan duniya, \q2 za a ga jini da wuta da murtukewar hayaƙi. \q1 \v 31 Rana za tă duhunta \q2 wata kuma yă zama jini \q2 kafin isowar babbar ranan nan mai banrazana ta \nd Ubangiji\nd*. \q1 \v 32 Amma dukan waɗanda suka nemi \q2 \nd Ubangiji\nd* za su tsira. \q1 Kamar yadda \nd Ubangiji\nd* ya ce, \q2 gama a Dutsen Sihiyona da Urushalima \q1 akwai ceto, \q2 a cikin waɗannan da \nd Ubangiji\nd* ya kira. \c 3 \s1 An shari’anta al’ummai \q1 \v 1 “A waɗancan kwanaki da kuma a wancan lokaci, \q2 sa’ad da zan maido da arzikin Yahuda da Urushalima, \q1 \v 2 zan tattara dukan al’ummai \q2 in kuma kawo su Kwarin Yehoshafat\f + \fr 3.2 \fr*\ft Yehoshafat yana nufin \+nd Ubangiji\+nd* ya shari’anta; haka ma a aya 12.\ft*\f* \q1 Can zan yi musu shari’a \q2 game da gādona, mutanena Isra’ila, \q1 gama sun warwatsar da mutanena a cikin al’ummai \q2 sun kuma raba ƙasata. \q1 \v 3 Sun jefa ƙuri’a a kan mutanena \q2 suna kuma sayar da yara maza don karuwanci, \q1 sun sayar da ’yan matan domin ruwan inabi \q2 wanda za su sha. \p \v 4 “Yanzu mene ne damuwarku da ni, ya Taya da Sidon da kuma dukan mazaunan yankunan Filistiya? Kuna ƙoƙari ku sāka mini don abin da na yi ne? In kuna sāka mini ne, to, da gaggawa zan mayar muku da sakayya a kanku. \v 5 Gama kun kwashe azurfata da zinariyata kun kuma washe dukiyata mafi kyau kun kai cikin haikalinku. \v 6 Kun sayar da mutanen Yahuda da na Urushalima ga mutanen Hellenawa, don ku aika da su nesa da ƙasarsu. \p \v 7 “Duba, zan dawo da su daga wuraren da kuka sayar da su, in kuma yi muku abin da kuka yi musu. \v 8 Zan sayar da ’ya’yanku maza da mata ga mutanen Yahuda, su kuma za su sayar da su ga mutanen Sabenawa, al’umma da take nesa da ku.” \nd Ubangiji\nd* ya faɗa. \q1 \v 9 Ku yi shelar wannan ga al’ummai. \q2 Ku yi shirin yaƙi! \q1 Ku tā da jarumawa! \q2 Bari mayaƙa su ja kusa su kai hari. \q1 \v 10 Ku bubbuge garemaninku su zama takuba \q2 da kuma laujenku su zama māsu. \q1 Bari raunana su ce, \q2 “Ni mai ƙarfi ne!” \q1 \v 11 Ku gaggauta, dukanku al’ummai daga kowane ɓangare, \q2 ku tattaru a can. \b \q1 Ka sauko da mayaƙanka, ya \nd Ubangiji\nd*! \b \q1 \v 12 “Bari a tā da dukan al’ummai; \q2 bari su kutsa zuwa Kwarin Yehoshafat \q1 gama a can zan zauna \q2 in shari’anta dukan al’ummai daga kowane ɓangare. \q1 \v 13 Ku fito da lauje, \q2 gama girbi ya nuna. \q1 Ku zo, ku tattaka inabin, \q2 gama wurin matsewar ruwan inabi ya cika \q2 randunan tarawa kuma sun cika har suna zuba, \q1 muguntarsu da girma take!” \b \q1 \v 14 Dubun dubbai \q2 suna a cikin kwarin yanke shawara! \q1 Gama ranar \nd Ubangiji\nd* ta yi kusa \q2 a cikin kwarin yanke shawara. \q1 \v 15 Za a duhunta rana da wata, \q2 taurari kuma ba za su ba da haske ba. \q1 \v 16 \nd Ubangiji\nd* zai yi ruri daga Sihiyona \q2 tsawa kuma daga Urushalima; \q1 duniya da sararin sama za su yi rawan jiki. \q1 Amma \nd Ubangiji\nd* zai zama mafakar mutanensa, \q2 mafaka ga mutanensa Isra’ila. \s1 Albarka domin mutanen Allah \q1 \v 17 “Sa’an nan za ku san cewa ni, \nd Ubangiji\nd* Allahnku, \q2 ina zaune a Sihiyona, dutsena mai tsarki. \q1 Urushalima za tă zama mai tsarki; \q2 baƙi ba za su ƙara mamaye ta ba. \b \q1 \v 18 “A wannan rana duwatsu za su ɗiga da sabon ruwan inabi, \q2 tuddai kuma za su malmalo madara; \q2 dukan rafuffukan Yahuda za su yi ta gudano da ruwa. \q1 Maɓulɓula kuma za tă fito daga gidan \nd Ubangiji\nd* \q2 haka ma ruwa a kwarin itatuwan ƙirya.\f + \fr 3.18 \fr*\ft Ko kuwa \ft*\fqa kwarin Shittim\fqa*\f* \q1 \v 19 Amma Masar za tă zama kango, \q2 Edom kuma hamada marar amfani, \q1 saboda kama-karyar da aka yi wa mutanen Yahuda, \q2 a ƙasar da aka zub da jinin marasa laifi. \q1 \v 20 Za a zauna a Yahuda har abada \q2 Urushalima kuma daga tsara zuwa tsara. \q1 \v 21 Alhakin jininsu, wanda ban gafarta ba, \q2 zan gafarta.” \b \qc \nd Ubangiji\nd* yana zama a Sihiyona!