\id AMO - Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ \ide UTF-8 \h Amos \toc1 Amos \toc2 Amos \toc3 Amos \mt1 Amos \c 1 \p \v 1 Kalmomin Amos, ɗaya daga cikin makiyayan Tekowa, abubuwan da ya gani game da Isra’ila shekaru biyu kafin a yi girgizar ƙasa, a lokacin da Uzziya yake sarkin Yahuda, Yerobowam ɗan Yowash kuma yake sarkin Isra’ila. \b \b \p \v 2 Ya ce, \q1 “\nd Ubangiji\nd* ya yi ruri daga Sihiyona \q2 ya kuma yi tsawa daga Urushalima; \q1 wuraren kiwo duk sun bushe, \q2 dutsen Karmel kuma ya yi yaushi.” \s1 Hukunci a kan maƙwabtan Isra’ila \p \v 3 Ga abin da \nd Ubangiji\nd* ya ce, \q1 “Saboda zunubai uku na Damaskus, \q2 har guda huɗu ma, ba zan fasa hukunta su ba. \q1 Domin sun ci zalunci Gileyad \q2 zalunci mai tsanani, \q1 \v 4 zan sa wuta a gidan Hazayel, \q2 da za tă ƙona kagarun Ben-Hadad. \q1 \v 5 Zan kakkarye ƙofofin Bet-Damaskus; \q2 zan hallaka sarkin da yake cikin\f + \fr 1.5 \fr*\ft Ko kuwa \ft*\fqa mazaunan\fqa*\f* Kwarin Awen\f + \fr 1.5 \fr*\fq Awen \fq*\ft yana nufin \ft*\fqa mugunta.\fqa*\f* \q1 da kuma mai riƙe da sandar mulkin Bet-Eden. \q2 Mutanen Aram za su je bauta a ƙasar Kir,” \q2 in ji \nd Ubangiji\nd*. \p \v 6 Ga abin da \nd Ubangiji\nd* ya ce, \q1 “Saboda zunubai uku na Gaza, \q2 har guda huɗu ma, ba zan fasa hukunta su ba. \q1 Don sun kwashe al’umma gaba ɗaya \q2 sun sayar wa Edom, \q1 \v 7 Zan aika da wuta a katangar Gaza \q2 ta ƙone duk kagarunta. \q1 \v 8 Zan hallaka sarkin\f + \fr 1.8 \fr*\ft Ko kuwa \ft*\fqa mazaunan\fqa*\f* Ashdod \q2 da kuma mai riƙe da sandar mulki na Ashkelon. \q1 Zan hukunta Ekron, \q2 har sai dukan Filistiyawa sun mutu,” \q2 in ji \nd Ubangiji\nd* Mai Iko Duka. \p \v 9 Ga abin da \nd Ubangiji\nd* ya ce, \q1 “Saboda zunubai uku na Taya, \q2 har guda huɗu ma, ba zan fasa hukunta su ba. \q1 Don sun kwashe al’umma gaba ɗaya sun kai su bauta a Edom, \q2 ba su kula da yarjejjeniyar da aka yi ta zama kamar ’yan’uwa ba, \q1 \v 10 zan aika da wuta a Taya, \q2 da za tă ƙone kagarunta.” \p \v 11 Ga abin da \nd Ubangiji\nd* ya ce, \q1 “Saboda zunubai uku na Edom, \q2 har guda huɗu ma, ba zan fasa hukunta shi ba. \q1 Don ya fafari ɗan’uwansa da takobi, \q2 babu tausayi, \q1 domin ya ci gaba da fusata \q2 bai yarda yă huce daga fushinsa ba. \q1 \v 12 Zan aika wuta a Teman \q2 da za tă ƙone kagarun Bozra.” \p \v 13 Ga abin da \nd Ubangiji\nd* ya ce, \q1 “Saboda zunubai uku na Ammon, \q2 har guda huɗu ma, ba zan fasa hukunta shi ba. \q1 Don ya tsaga cikin matan Gileyad masu juna biyu \q2 don kawai yă ƙwace ƙasar. \q1 \v 14 Zan sa wuta a katangar Rabba \q2 da za tă ƙone kagarunta \q1 za a yi kururuwa a ranar yaƙi, \q2 faɗan kuwa zai yi rugugi kamar hadiri. \q1 \v 15 Sarkinta\f + \fr 1.15 \fr*\ft Ko kuwa \ft*\fqa Molek; \fqa*\ft Ibraniyawa \ft*\fqa malkam\fqa*\f* zai je bauta, \q2 shi da ma’aikatansa,” \q2 in ji \nd Ubangiji\nd*. \c 2 \p \v 1 Ga abin da \nd Ubangiji\nd* ya ce, \q1 “Saboda zunubai uku na Mowab, \q2 har guda huɗu ma, ba zan fasa hukunta su ba. \q1 Gama ya ƙone ƙasusuwan sarkin Edom \q2 suka zama sai ka ce toka. \q1 \v 2 Zan sa wuta a Mowab \q2 da za tă ƙone kagarun Keriyot\f + \fr 2.2 \fr*\ft Ko kuwa \ft*\fqa na biranenta\fqa*\f* \q1 Mowab za tă gangara cikin hayaniya mai girma \q2 cikin kururuwar yaƙi da kuma ƙarar ƙaho. \q1 \v 3 Zan hallaka mai mulkinta \q2 zan kuma kashe shugabanninta.” \p \v 4 Ga abin da \nd Ubangiji\nd* ya ce, \q1 “Saboda zunubai uku na Yahuda, \q2 har guda huɗu ma, ba zan fasa hukunta su ba. \q1 Gama sun ƙi bin dokar \nd Ubangiji\nd* \q2 ba su kuma yi biyayya da ƙa’idodinsa ba, \q1 domin allolin ƙarya sun ruɗe su, \q2 allolin da kakanninsu suka bauta. \q1 \v 5 Zan sa wuta a Yahuda \q2 da za tă ƙone kagarun Urushalima.” \s1 Hukunci a kan Isra’ila \p \v 6 Ga abin da \nd Ubangiji\nd* ya ce, \q1 “Saboda zunubai uku na Isra’ila, \q2 har guda huɗu ma, ba zan fasa hukunta su ba. \q1 Don sun sayar da adalai waɗanda \q2 suka kāsa biyan bashinsu. \q1 Sun kuma sayar da matalauta \q2 waɗanda bashinsu bai ma kai ko kuɗin bi-labi ba. \q1 \v 7 Sun tattake kawunan matalauta \q2 kamar yadda suke taka laka \q2 suka kuma danne wa marasa galihu gaskiya. \q1 Uba da ɗa su na kwana da yarinya guda, \q2 suna kuma ɓata sunana mai tsarki. \q1 \v 8 Suna kwanciya kurkusa da kowane bagade \q2 a kan tufafin da suka karɓe jingina. \q1 A gidajen allolinsu \q2 sukan sha ruwan inabin da suka karɓo daga wurin waɗanda suka ci wa tara. \b \q1 \v 9 “Na hallaka mutumin Amoriyawa a gabansu, \q2 ko da yake ya yi dogo kamar itacen al’ul \q2 kuma mai ƙarfi kamar itacen oak. \q1 Na hallaka ’ya’yan itatuwansa daga sama, \q2 da kuma jijiyoyinsa daga ƙasa. \q1 \v 10 Na fitar da ku daga ƙasar Masar, \q2 na kuma bishe ku tsawon shekaru arba’in a cikin hamada \q2 don in ba ku ƙasar Amoriyawa. \b \q1 \v 11 “Na kuma tā da annabawa daga cikin ’ya’yanku maza \q2 waɗansu kuma su zama keɓaɓɓu daga cikin samarinku. \q1 Ba haka ba ne, mutanen Isra’ila?” \q2 In ji \nd Ubangiji\nd*. \q1 \v 12 “Amma kuka sa keɓaɓɓun suka sha ruwan inabi \q2 kuka kuma umarci annabawa kada su yi annabci. \b \q1 \v 13 “Saboda haka, yanzu zan murƙushe ku \q2 kamar yadda amalanke yakan murƙushe sa’ad da aka yi masa labtun hatsi. \q1 \v 14 Masu gudu da sauri ba za su tsira ba, \q2 masu ƙarfi ba za su iya yin amfani da ƙarfinsu ba, \q2 jarumi kuma ba zai iya ceton ransa ba. \q1 \v 15 ’Yan baka ba za su iya dāgewa ba, \q2 masu saurin gudu ba za su tsira ba \q2 mahayin dawakai kuma ba zai tsere da ransa ba. \q1 \v 16 Ko jarumawa mafi jaruntaka \q2 za su gudu tsirara a ranan nan,” \q2 in ji \nd Ubangiji\nd*. \c 3 \s1 An kira shaidu a kan Isra’ila \p \v 1 Ku ji wannan maganar da \nd Ubangiji\nd* ya yi game da ku, ya ku jama’ar Isra’ila, a kan dukan iyalin da na fitar daga Masar. \q1 \v 2 “Ku ne kaɗai na zaɓa \q2 cikin dukan al’umman duniya; \q1 saboda haka zan hukunta ku \q2 saboda dukan zunubanku.” \b \q1 \v 3 Mutum biyu za su iya yin tafiya tare \q2 in ba su yarda su yi haka ba? \q1 \v 4 Zaki yakan yi ruri a jeji \q2 in bai sami kama nama ba? \q1 Zai yi gurnani a cikin kogonsa \q2 in bai kama kome ba? \q1 \v 5 Tsuntsu yakan fāɗa a tarko a ƙasa \q2 inda ba a sa tarko ba, \q1 ko tarko yakan zargu daga ƙasa \q2 in ba abin da ya taɓa shi? \q1 \v 6 Idan aka busa ƙaho a ciki birni \q2 mutane ba sa yin rawar jiki? \q1 Sa’ad da bala’i ya auko wa birni, \q2 ba \nd Ubangiji\nd* ne ya sa a kawo shi ba? \b \q1 \v 7 Ba shakka, \nd Ubangiji\nd* Mai Iko Duka ba ya yin wani abu \q2 ba tare da ya sanar wa bayinsa annabawa ba. \b \q1 \v 8 Zaki ya yi ruri, \q2 wa ba zai tsorata ba? \q1 \nd Ubangiji\nd* Mai Iko Duka ya yi magana, \q2 wa ba zai yi annabci ba? \b \q1 \v 9 Ku yi shela ga kagarun Ashdod \q2 da kuma ga kagarun Masar. \q1 “Ku tara kanku a tuddan Samariya; \q2 ku ga rashin jituwar da take a cikinta, \q2 da kuma zaluncin da ake yi a cikin mutanenta.” \b \q1 \v 10 “Ba su ma san yadda za su yi abin da yake daidai ba,” \q2 in ji \nd Ubangiji\nd*, \q2 “sun ɓoye ganima da abubuwan da suka washe a cikin kagarunsu.” \p \v 11 Saboda haka ga abin da \nd Ubangiji\nd* Mai Iko Duka ya ce, \q1 “Abokin gāba zai ƙwace ƙasar, \q2 zai saukar da mafakarku, \q2 zai washe kagarunku.” \p \v 12 Ga abin da \nd Ubangiji\nd* ya ce, \q1 “Kamar yadda makiyayi yakan ceci daga bakin zaki \q2 ƙasusuwa ƙafafu biyu kawai ko kunne ɗaya, \q2 haka za a ceci Isra’ilawa, \q1 masu zama a Samariya \q2 da kan gado kawai \q2 da kuma a ɗan ƙyalle\f + \fr 3.12 \fr*\ft Ma’anar kalmar Ibraniyancin nan babu tabbas.\ft*\f* a kan dogayen kujerunsu.\f + \fr 3.12 \fr*\ft Ko kuwa \ft*\fqa Za a ceci Isra’ilawa / waɗanda suke zama a Samariya / a gefen gadajensu / da kuma a Damaskus kan kujerunsu\fqa*\f*” \p \v 13 “Ku ji wannan ku kuma yi wa gidan Yaƙub gargaɗi,” in ji \nd Ubangiji\nd*, \nd Ubangiji\nd* Allah Maɗaukaki. \q1 \v 14 “A ranar da zan hukunta Isra’ila saboda zunubanta, \q2 zan hallaka bagadan Betel; \q1 za a yayyanka ƙahonin bagadan \q2 za su fāɗa ƙasa \q1 \v 15 Zan rushe gidan rani \q2 da na damina; \q2 gidajen da aka yi musu ado da hauren giwa za a rushe su \q2 haka ma duk za a rurrushe manyan gidaje,” \q2 in ji \nd Ubangiji\nd*. \c 4 \s1 Isra’ila ba ta koma ga Allah ba \q1 \v 1 Ku kasa kunne ga wannan, ya ku shanun Bashan a kan Dutsen Samariya, \q2 ku matan da kuke cin zalin matalauta, kuke kuma danne matalauta, \q2 kuna kuma ce wa mazanku, “Ku kawo mana abin sha!” \q1 \v 2 \nd Ubangiji\nd* Mai Iko Duka ya rantse da tsarkinsa. \q2 “Tabbatacce lokaci yana zuwa \q1 da za a jawo ku da ƙugiyoyi, \q2 na ƙarshenku za a kama da ƙugiyar kifi. \q1 \v 3 Dukanku za ku wuce ta kai tsaye \q2 ta inda katangar ta tsage, \q2 za a jefar da ku a Harmon,”\f + \fr 4.3 \fr*\ft Rubuce-rubucen hannu na Masoretik; da ɓangare dabam na kalmar Ibraniyanci (dubi Seftuwajin) \ft*\fqa waje, ya dutsen danniya\fqa*\f* \q2 in ji \nd Ubangiji\nd*. \q1 \v 4 “Ku tafi Betel ku yi ta aikata zunubi; \q2 ku je Gilgal ku ƙara yin zunubi. \q1 Ku kawo hadayunku kowace safiya, \q2 zakkarku kowace shekara uku.\f + \fr 4.4 \fr*\ft Ko kuwa \ft*\fqa zakka a rana ta uku\fqa*\f* \q1 \v 5 Ku ƙona burodinku mai yisti kamar hadaya ta godiya, \q2 ku yi fariya game da hadayunku na yarda rai, \q1 ku yi taƙama game da su, ya ku Isra’ilawa, \q1 gama abin da kuke jin daɗin aikata ke nan,” \q2 in ji \nd Ubangiji\nd* Mai Iko Duka. \b \q1 \v 6 “Na bar ku da yunwa\f + \fr 4.6 \fr*\ft Ibraniyanci \ft*\fqa ku da tsabtar haƙora\fqa*\f* a kowace birni, \q2 da kuma rashin abinci a kowane gari, \q2 duk da haka ba ku juyo gare ni ba,” \q2 in ji \nd Ubangiji\nd*. \b \q1 \v 7 “Na kuma hana muku ruwan sama \q2 tun shuke-shuken suna wata uku kafin lokacin girbi. \q1 Na sa aka yi ruwan sama a wani gari, \q2 sai na hana a yi a wani gari. \q1 Wata gona ta sami ruwan sama; \q2 wata gona kuma ta bushe. \q1 \v 8 Mutane suna tangaɗi daga gari zuwa gari suna neman ruwa \q2 amma ba su sami isashen ruwan sha ba, \q2 duk da haka ba ku juyo gare ni ba,” \q2 in ji \nd Ubangiji\nd*. \b \q1 \v 9 “Sau da yawa na ɓata gonakinku \q2 da fumfuna da kuma cuta. \q2 Fāri suka cinye itatuwanku na inabi da na ɓaure, da na zaitun \q1 duk da haka ba ku juyo gare ni ba,” \q2 in ji \nd Ubangiji\nd*. \b \q1 \v 10 “Na aiko muku annoba \q2 yadda na yi a Masar. \q1 Na karkashe samarinku da takobi, \q2 tare da kamammun dawakanku. \q1 Na cika hancinku da warin sansaninku, \q2 duk da haka ba ku juyo gare ni ba” \q2 in ji \nd Ubangiji\nd*. \b \q1 \v 11 “Na hallaka waɗansunku \q2 kamar\f + \fr 4.11 \fr*\ft Ibraniyanci \ft*\fqa Allah\fqa*\f* yadda na hallaka Sodom da Gomorra. \q1 Kuna kama da itace mai cin wutar da na cire daga cikin wuta, \q2 duk da haka ba ku juyo gare ni ba,” \q2 in ji \nd Ubangiji\nd*. \b \q1 \v 12 “Saboda haka ga abin da zan yi da ku, ya Isra’ila, \q2 don kuwa zan yi muku haka, \q2 sai ku yi shirin gamuwa da Allahnku, ya Isra’ila.” \b \q1 \v 13 Shi wanda ya yi duwatsu, \q2 ya halicci iska, \q2 ya kuma bayyana wa mutum tunaninsa, \q1 shi wanda ya juya safiya ta zama duhu \q2 yana takawa a wurare masu tsawo na duniya, \q2 \nd Ubangiji\nd* Allah Maɗaukaki ne sunansa. \c 5 \s1 Makoki da kuma kira ga tuba \p \v 1 Ku ji wannan magana, ya gidan Isra’ila, ina makokin nan dominku. \q1 \v 2 “Budurwa Isra’ila ta fāɗi, \q2 ba za tă ƙara tashi ba, \q1 an yashe ta a ƙasarta, \q2 ba wanda zai ɗaga ta.” \p \v 3 Ga abin da \nd Ubangiji\nd* Mai Iko Duka ya ce, \q1 “Birnin da ta fitar da masu ƙarfi dubbai don Isra’ila \q2 guda ɗari kaɗai za su dawo; \q1 garin da ya fitar da masu ƙarfi ɗari kuwa \q2 goma kaɗai za su dawo.” \p \v 4 Ga abin da \nd Ubangiji\nd* ya ce wa gidan Isra’ila. \q1 “Ku neme ni ku rayu; \q2 \v 5 kada ku nemi Betel, \q1 kada ku je Gilgal, \q2 kada ku yi tafiya zuwa Beyersheba. \q1 Gama ba shakka Gilgal za tă tafi bauta, \q2 za a kuwa mai da Betel ba kome ba.”\f + \fr 5.5 \fr*\ft Ko kuwa \ft*\fqa baƙin cikin; \fqa*\ft Ko kuwa \ft*\fqa mugunta; \fqa*\ft Da Ibraniyanci \ft*\fqa awen, \fqa*\ft kwatanci ga Bet Awen (wani sunan reni don Betel).\ft*\f* \q1 \v 6 Ku nemi \nd Ubangiji\nd* ku kuma rayu, \q2 ko kuwa zai ratsa yă share gidan Yusuf kamar wuta; \q1 zai cinye \q2 Betel kuwa ba zai sami wanda zai kashe ta ba. \b \q1 \v 7 Ku ne masu mai da gaskiya ta koma ɗaci \q2 ku kuma zubar da adalci. \b \q1 \v 8 (Shi wanda ya yi Taurarin nan da ake ce Kaza da ’Ya’yanta da kuma Mai Farauta da Kare, \q2 wanda ya mai da duhu ya zama haske \q2 ya kuma baƙanta rana ta zama dare, \q1 yakan kwashe ruwan teku \q2 ya zubar a ƙasa, \q2 \nd Ubangiji\nd* ne sunansa, \q1 \v 9 yakan kawo hallaka a mafaka mai ƙarfi \q2 yakan kuma mai da birnin mai katanga ya zama kufai). \b \q1 \v 10 Ba ku son mai yin gaskiya a ɗakin shari’a \q2 kuna ƙin mai faɗar gaskiya. \b \q1 \v 11 Kuna matsa wa matalauta \q2 kuna sa su dole su ba ku hatsi. \q1 Saboda haka, ko da yake kun gina gidajen duwatsu, \q2 ba za ku zauna a cikinsu ba; \q1 ko da yake kun nome gonaki masu kyau, \q2 ba za ku sha ruwan inabinsu ba. \q1 \v 12 Gama na san yawan laifofinku \q2 da kuma girman zunubanku. \b \q1 Kuna danne masu adalci kuna kuma cin hanci \q2 kuna kuma hana a yi wa matalauta shari’ar adalci a majalisa. \q1 \v 13 Saboda haka mai hankali yakan yi shiru a lokuta kamar haka, \q2 gama lokutan mugaye ne. \b \q1 \v 14 Ku yi nagarta, ba mugunta ba; \q2 don ku rayu \q1 sa’an nan \nd Ubangiji\nd* Allah Maɗaukaki zai kasance da ku, \q2 kamar yadda kuka ce zai yi. \q1 \v 15 Ku ƙi mugunta, ku ƙaunaci nagarta; \q2 ku dinga yin shari’ar gaskiya a ɗakunan shari’a. \q1 Mai yiwuwa \nd Ubangiji\nd* Allah Maɗaukaki zai ji tausayin \q2 raguwar Yusuf. \p \v 16 Saboda haka ga abin da Ubangiji, \nd Ubangiji\nd* Allah Maɗaukaki yana cewa, \q1 “Za a yi kururuwa a dukan tituna \q2 a kuma yi kuka don azaba a dukan wuraren da jama’a sukan taru. \q1 Za a yi kira ga manoma su yi kuka \q2 masu makoki kuma su yi kuka. \q1 \v 17 Za a yi kuka a dukan gonakin inabi, \q2 gama zan ratsa a cikinku,” \q2 in ji \nd Ubangiji\nd*. \s1 Ranar \nd Ubangiji\nd* \q1 \v 18 Kaitonku masu son \q2 ganin ranar \nd Ubangiji\nd*! \q1 Don me kuke son ganin ranar \nd Ubangiji\nd*? \q2 Za a duhunta ranan nan, ba haske ba. \q1 \v 19 Za ku zama kamar mutanen da suka guje wa zaki \q2 sai suka fāɗa a hannun beyar, \q1 ko kuma kamar wanda ya shiga gida \q2 ya dāfa hannu a bango \q2 sai maciji ya sare shi. \q1 \v 20 Ashe, ranar \nd Ubangiji\nd* ba duhu ba ce, a maimakon haske, \q2 duhu wuluk, ba tare da ko ɗan haske ba. \b \q1 \v 21 “Na ƙi, ina kuma ƙyamar bukukkuwanku na addini; \q2 ba na son ganin tarurrukanku. \q1 \v 22 Ko da kun kawo mini hadayu na ƙonawa da kuma hadayu na hatsi, \q2 ba zan karɓa ba. \q1 Ko da kun kawo zaɓaɓɓun hadayu na zumunta, \q2 ba zan ɗauke su a bakin kome ba. \q1 \v 23 Ku tashi daga nan da surutan waƙoƙinku! \q2 Ba zan saurari kaɗe-kaɗe da bushe bushenku ba. \q1 \v 24 Amma bari gaskiya ta kwararo kamar kogi, \q2 adalci kuma kamar rafin da ba ya taɓa bushewa! \b \q1 \v 25 “Kun kawo mini hadayu da sadakoki \q2 shekaru arba’in a cikin jeji, ya ku gidan Isra’ila? \q1 \v 26 Kun ɗaga masujadar sarkinku, \q2 siffofin gumakanku, \q2 tauraron allahnku,\f + \fr 5.26 \fr*\ft Ko kuwa \ft*\fqa ɗaga Sakkut sarkinku da Kaiwan gumakanku, tauraron da suke allolinku; \fqa*\ft Seftuwajin \ft*\fqa ɗaga masujadar Molek da tauraro allahnku Refan, gumakansu\fqa*\f* \q2 wanda kuka yi wa kanku. \q1 \v 27 Saboda haka zan tura ku zaman bauta gaba da Damaskus,” \q2 in ji \nd Ubangiji\nd*, wanda sunansa ne Allah Mai Iko. \c 6 \s1 Kaito ga zaman sakewa \q1 \v 1 Taku ta ƙare, ku da kuke zaman sakewa a Sihiyona, \q2 da ku waɗanda kuke ji zama a Dutsen Samariya lafiya ne, \q1 ku manyan mutanen ƙasar da take sananniya, \q2 waɗanda mutanen Isra’ila suke zuwa! \q1 \v 2 Ku je Kalne ku dube ta; \q2 ku wuce daga can zuwa Hamat-rabba, \q2 sa’an nan ku gangara zuwa Gat a Filistiya. \q1 Sun fi masarautunku biyu ne? \q2 Ƙasarsu ta fi taku girma? \q1 \v 3 Kuna ƙoƙari ku kauce wa wannan muguwar rana \q2 kuna kuma jawo mulkin tashin hankali kusa. \q1 \v 4 Kuna kwanciya a kan gadajen da aka yi musu shimfiɗar hauren giwa \q2 kuna mimmiƙe a kan kujerunku. \q1 Kuna cin naman ƙibabbun raguna \q2 da na ƙosassun ’yan maruƙa. \q1 \v 5 Kuna kaɗa molayenku yadda Dawuda ya yi \q2 kuna ƙirƙiro waƙoƙi a kan kayan kaɗe-kaɗe. \q1 \v 6 Da manyan kwanoni kuke shan ruwan inabi \q2 kuna kuma shafa mai mafi kyau, \q2 amma ba kwa baƙin ciki game da kangon da Yusuf ya zama. \q1 \v 7 Saboda haka za ku zama na farkon da za su tafi zaman bauta; \q2 bukukkuwanku da shagulgulanku za su ƙare. \s1 \nd Ubangiji\nd* yana ƙyamar girmankan Isra’ila \p \v 8 \nd Ubangiji\nd* Mai Iko Duka da kansa ya rantse, \nd Ubangiji\nd* Allah Maɗaukaki ya furta, \q1 “Ina ƙyamar girman kan Yaƙub, \q2 ba na kuma son kagarunsa; \q1 zan ba da birnin \q2 da duk abin da yake cikinta.” \p \v 9 Ko da mutum goma ne suka ragu a gida guda, su ma za su mutu. \v 10 In kuma wani dangi ya shiga don yă fitar da gawawwakin yă ƙone ya kuwa tambayi wani wanda yake ɓoye a can, yana cewa, “Akwai wani tare da kai?” Ya kuwa ce, “Babu,” sai yă ce, “Kul! Kada mu ambaci sunan \nd Ubangiji\nd*.” \q1 \v 11 Gama \nd Ubangiji\nd* ya ba da umarni, \q2 zai kuma ragargaza babban gidan nan kucu-kucu \q2 ƙaramin gidan kuwa zai yi rugu-rugu da shi. \b \q1 \v 12 Dawakai sukan yi gudu a kan duwatsu? \q2 Wani yana iya yin noma a teku da shanun noma? \q1 Amma ga shi kun mai da gaskiya ta zama dafi \q2 amfanin adalci kuma ya zama ɗaci, \q1 \v 13 ku da kuke murna saboda an ci Lo Debar\f + \fr 6.13 \fr*\fq Lo Debar \fq*\ft yana nufin \ft*\fqa wofi.\fqa*\f* da yaƙi \q2 kuka kuma ce, “Ba da ƙarfinmu ne muka ƙwace Karnayim\f + \fr 6.13 \fr*\fq Karnayim \fq*\ft yana nufin \ft*\fqa ƙahoni; \fqa*\fqa ƙaho \fqa*\ft a nan yana a matsayin ƙarfi.\ft*\f* ba?” \b \q1 \v 14 Gama \nd Ubangiji\nd* Allah Maɗaukaki ya ce, \q2 “Zan sa wata ƙasa ta tayar muku, ya ku gidan Isra’ila, \q1 wadda za tă matsa muku tun \q2 daga Lebo\f + \fr 6.14 \fr*\ft Ko kuwa \ft*\fqa daga mashigi zuwa\fqa*\f* Hamat zuwa kwarin Araba.” \c 7 \s1 Fāri, wuta, da igiyar gwaji \p \v 1 Ga abin da \nd Ubangiji\nd* Mai Iko Duka ya nuna mini. \nd Ubangiji\nd* yana shirya cincirindon fāri bayan da aka ƙarasa yankan rabon hatsin da yake na sarki, hatsi na biyu kuma yake tohuwa. \v 2 Sa’ad da suka cinye kome, sai na yi kira, na ce, “\nd Ubangiji\nd* Mai Iko Duka, ka gafarta! Ta yaya Yaƙub zai tsira? Ga shi ɗan ƙarami ne!” \p \v 3 Saboda haka sai \nd Ubangiji\nd* ya dakatar da nufinsa. \p “Wannan ba zai faru ba,” in ji \nd Ubangiji\nd*. \p \v 4 Ga abin da \nd Ubangiji\nd* Mai Iko Duka ya nuna mini. \nd Ubangiji\nd* Mai Iko Duka yana shirin hukunta da wuta; wutar ta ƙone teku ta kuma ƙone ƙasa. \v 5 Sai na yi kira, na ce, “\nd Ubangiji\nd* Mai Iko Duka, ina roƙonka ka dakata! Ta yaya Yaƙub zai tsira? Ga shi ɗan ƙarami ne!” \p \v 6 Saboda haka sai \nd Ubangiji\nd* ya dakatar da nufinsa. \p “Wannan ma ba zai faru ba,” in ji \nd Ubangiji\nd* Mai Iko Duka. \b \p \v 7 Ga abin da ya nuna mini. Ubangiji yana tsaye kusa da bangon da aka gina, bisa ga awon igiyar gwada gini, da kuma magwaji a hannunsa. \v 8 Sai \nd Ubangiji\nd* ya tambaye ni, “Me kake gani, Amos?” \p Sai na amsa, “Igiyar gwada gini.” \p Sa’an nan Ubangiji ya ce, “Duba, zan sa igiyan nan a cikin mutanena Isra’ila; ba zan ƙara barinsu ba. \q1 \v 9 “Za a hallakar da wuraren sujada na Ishaku \q2 kuma tsarkakan wurare na Isra’ila za su zama kango; \q2 da takobina zan tayar wa gidan Yerobowam.” \s1 Amos da Amaziya \p \v 10 Sai Amaziya firist na Betel ya aika da saƙo zuwa wurin Yerobowam sarkin Isra’ila. “Amos yana shirya maka maƙarƙashiya a tsakiyar Isra’ila. Ƙasar ba za tă iya ɗauka abubuwan da yake faɗi ba. \v 11 Gama ga abin da Amos yake cewa, \q1 “ ‘Yerobowam zai mutu ta wurin takobi, \q2 kuma tabbatacce Isra’ila za su tafi zaman bauta, \q2 nesa da ainihin ƙasarsu.’ ” \p \v 12 Sai Amaziya ya ce wa Amos, “Tafi daga nan, mai duba kawai! Koma ƙasar Yahuda. Ka nemi abin zaman garinka a can ka kuma yi annabcinka a can. \v 13 Kada ka ƙara yin annabci a Betel, gama nan wuri mai tsarki ne na sarki da kuma haikalin ƙasar.” \p \v 14 Amos ya amsa wa Amaziya, “Ni ba annabi ba ne ko ɗan annabi, amma ni makiyayi ne, kuma ina lura da itatuwan al’ul. \v 15 Amma \nd Ubangiji\nd* ya ɗauke ni daga kiwon dabbobi ya ce mini, ‘Je ka, ka yi wa mutanena Isra’ila annabci.’ \v 16 Yanzu fa, sai ka ji maganar \nd Ubangiji\nd*. Ka ce, \q1 “ ‘Kada in yi annabci a kan Isra’ila, \q2 kuma in daina yin wa’azi a kan gidan Ishaku.’ \p \v 17 “Saboda haka ga abin da \nd Ubangiji\nd* ya ce, \q1 “ ‘Matarka za tă zama karuwa a cikin birni, \q2 kuma da takobi za a kashe ’ya’yanka maza da mata. \q1 Za a auna ƙasarka a kuma raba ta, \q2 kai kuma za ka mutu a ƙasar arna.\f + \fr 7.17 \fr*\ft Da Ibraniyanci \ft*\fqa marasa tsabta\fqa*\f* \q1 Ba shakka Isra’ila za su tafi zaman bauta, \q2 nesa da ainihin ƙasarsu.’ ” \c 8 \s1 Kwandon nunannun ’ya’yan itace \p \v 1 Ga abin da \nd Ubangiji\nd* Mai Iko Duka ya nuna mini. \nd Ubangiji\nd* ya nuna mini kwandon nunannun ’ya’yan itace. \v 2 Ya yi tambaya ya ce, “Me ka gani Amos?” \p Sai na amsa na ce, “Kwandon nunannun ’ya’yan itace.” \p Sai \nd Ubangiji\nd* ya ce mini, “Lokaci ya yi wa mutanena Isra’ila da ba zan ƙara barinsu ba. \p \v 3 “A ranan nan,” in ji \nd Ubangiji\nd* Mai Iko Duka, “Waƙoƙin a haikali za su koma makoki.\f + \fr 8.3 \fr*\ft Ko kuwa \ft*\fqa “mawaƙar haikali za su yi makoki”\fqa*\f* Za a ga gawawwaki a ko’ina! Shiru!” \q1 \v 4 Ku ji wannan, ku da kuke tattake masu bukata \q2 kuka kori matalautan ƙasar. \p \v 5 Kuna cewa, \q1 “Yaushe Sabon Wata zai wuce \q2 don mu sayar da hatsi, \q1 Asabbaci ta wuce, \q2 don mu sayar da alkama?” \q1 Mu yi awo da ma’aunin zalunci \q2 mu ƙara kuɗin kaya \q2 mu kuma cutar da mai saya, \q1 \v 6 mu sayi matalauta da azurfa \q2 masu bukata kuma da takalmi, \q2 mu sayar da alkamar haɗe da yayi. \p \v 7 \nd Ubangiji\nd* ya rantse da Girman Yaƙub, “Ba zan taɓa mantawa da duk wani abin da suka yi ba. \q1 \v 8 “Shin, ƙasar ba za tă yi rawan jiki saboda wannan ba, \q2 kuma duk masu zama a cikinta ba za su yi makoki ba? \q1 Ƙasar duka za tă hau ta sauka kamar Nilu; \q2 za a dama ta sa’an nan ta nutse \q2 kamar kogin Masar. \p \v 9 “A wannan rana,” in ji \nd Ubangiji\nd* Mai Iko Duka, \q1 “Zan sa rana ta fāɗi da tsakar rana \q2 in kuma duhunta duniya da rana tsaka. \q1 \v 10 Zan mai da bukukkuwanku na addini su zama makoki \q2 kuma dukan waƙoƙinku su zama kuka. \q1 Zan sa dukanku ku sa rigunan makoki \q2 za ku kuma aske kawunanku. \q1 Zan sa wannan lokaci yă zama kamar lokacin da ake makokin ɗan tilon da ake da shi \q2 kuma ƙarshenta kamar rana mai ɗaci. \b \q1 \v 11 “Ranakun suna zuwa,” in ji \nd Ubangiji\nd* Mai Iko Duka, \q2 “sa’ad da zan aika da yunwa cikin ƙasar, \q1 ba yunwar abinci ko ta ƙishirwa ba, \q2 sai dai yunwa ta jin maganar \nd Ubangiji\nd*. \q1 \v 12 Mutane za su yi ta tangaɗi daga teku zuwa teku \q2 suna yawo daga arewa zuwa kudu, \q1 suna neman maganar \nd Ubangiji\nd*, \q2 amma ba za su samu ba. \p \v 13 “A wannan rana \q1 “kyawawan ’yan mata da kuma samari masu ji da ƙarfi \q2 za su suma don ƙishirwa. \q1 \v 14 Waɗanda suka yi rantsuwa da abin kunya\f + \fr 8.14 \fr*\ft Ko kuwa \ft*\fqa da Ashima; \fqa*\ft ko \ft*\fqa da gunki\fqa*\f* na Samariya, \q2 ko kuma su ce, ‘Muddin allahnku yana a raye, ya Dan,’ \q2 ko kuwa, ‘Muddin allahn\f + \fr 8.14 \fr*\ft Ko kuwa \ft*\fqa iko\fqa*\f* Beyersheba yana a raye,’ \q1 za su fāɗi, \q2 ba kuwa za su ƙara tashi ba.” \c 9 \s1 Za a hallaka Isra’ila \p \v 1 Na ga Ubangiji yana tsaye a gaban bagade, ya kuma ce, \q1 “Bugi kan ginshiƙan \q2 don madogaran ƙofa su girgiza. \q1 Saukar da su a kan dukan mutane; \q2 waɗanda ba su mutu ba zan kashe su da takobi. \q1 Ba mutum guda da zai tsere, \q2 babu wani da zai tsira. \q1 \v 2 Ko da sun tona rami kamar zurfin kabari, \q2 daga can hannuna zai fitar da su. \q1 Ko da sun hau can sama \q2 daga can zan sauko da su. \q1 \v 3 Ko da sun ɓuya a bisa Karmel, \q2 a can zan farauce su in cafko. \q1 Ko da sun ɓuya can ƙarƙashin teku, \q2 a can zan umarci maciji yă sare su. \q1 \v 4 Ko da abokan gābansu sun kore su zuwa zaman bauta, \q2 a can zan umarci takobi yă kashe su. \b \q1 “Zan sa musu ido \q2 don mugunta ba don alheri ba.” \b \q1 \v 5 Ubangiji, \nd Ubangiji\nd* Maɗaukaki, \q2 shi da yakan taɓa ƙasa sai ta narke, \q2 kuma dukan mazauna cikinta suna makoki, \q1 ƙasar gaba ɗaya takan hau ta kuma sauka kamar Nilu, \q2 sa’an nan ta nutse kamar kogin Masar, \q1 \v 6 shi da ya gina kyakkyawar fadarsa\f + \fr 9.6 \fr*\ft Ma’anar Ibraniyanci don wannan zance babu tabbas.\ft*\f* a cikin sammai \q2 ya kuma kafa harsashenta\f + \fr 9.6 \fr*\ft Ma’anar Ibraniyanci don wannan kalma babu tabbas.\ft*\f* a duniya, \q1 shi da yakan kira ruwan teku \q2 yă kuma kwarara su a bisa duniya, \q2 \nd Ubangiji\nd* ne sunansa. \b \q1 \v 7 “Ku ba Isra’ilawa ba ne, \q2 daidai gare ni kamar yadda Kushawa suke?”\f + \fr 9.7 \fr*\ft Wato, mutane daga yankin bisa na Nilu\ft*\f* \q2 In ji \nd Ubangiji\nd*. \q1 “Ban fito da Isra’ila daga Masar ba, \q2 Filistiyawa kuma daga Kaftor\f + \fr 9.7 \fr*\ft Wato, Kirit\ft*\f* \q2 Arameyawa kuma daga Kir ba? \b \q1 \v 8 “Tabbatacce idanun \nd Ubangiji\nd* Mai Iko Duka \q2 suna a kan mulkin nan mai zunubi. \q1 Zan hallaka shi \q2 daga fuskar duniya, \q1 duk da haka ba zan hallaka \q2 gidan Yaƙub ƙaƙaf ba,” \q2 in ji \nd Ubangiji\nd*. \q1 \v 9 “Gama zan ba da umarni, \q2 zan kuma tankaɗe gidan Isra’ila \q2 a cikin dukan ƙasashe \q1 kamar yadda ake tankaɗe hatsi a cikin matankaɗi \q2 kuma ko ƙwaya ɗaya ba za tă fāɗi a ƙasa ba. \q1 \v 10 Dukan masu zunubi a cikin mutanena \q2 za su mutu ta wurin takobi, \q1 wato, su masu cewa, \q2 ‘Masifa ba za tă fāɗo ko ta same mu ba.’ \s1 Maidowar Isra’ila \q1 \v 11 “A wannan rana zan maido \q2 da tentin Dawuda da ya fāɗi. \q1 Zan gyaggyara wuraren da suka yayyage, \q2 in kuma maido da kufansa \q2 in gina shi kamar yadda yake a dā, \q1 \v 12 domin su mallaki raguwar Edom \q2 da duk al’ummai da suke amsa sunana,”\f + \fr 9.12 \fr*\ft Da Ibraniyanci; Seftuwajin \ft*\fqa don raguwar mutane / da kuma dukan al’umman da ake kira da sunana za su nemi Ubangiji\fqa*\f* \q2 in ji \nd Ubangiji\nd* shi wanda zai yi waɗannan abubuwa. \p \v 13 “Ranaku suna zuwa, in ji \nd Ubangiji\nd*, \q1 “sa’ad da mai huɗa zai sha gaban mai girbi \q2 mai shuki kuma yă bi bayan mai matsin inabi. \q1 Sabon ruwan inabi zai ɗiga daga duwatsu \q2 yă kuma kwararo daga tuddai. \q2 \v 14 Zan dawo da waɗanda aka kai zaman bauta\f + \fr 9.14 \fr*\ft Ko kuwa \ft*\fqa zan maido da nasarar\fqa*\f* mutanena Isra’ila. \b \q1 “Za su sāke gina biranen da suke kango su kuma zauna a cikinsu. \q2 Za su shuka gonakin inabi su kuma sha ruwan inabinsu; \q2 za su yi lambuna su kuma ci amfaninsu. \q1 \v 15 Zan dasa Isra’ila a ƙasarsu, \q2 ba kuwa za a ƙara tumɓuke su \q2 daga ƙasar da na ba su ba,” \m in ji \nd Ubangiji\nd* Allahnku.